Hukumar Hisbah a Kano Ta Kama Fitacciyar Jarumar TikTok, Murja Kunya
- Jami'an hukumar Hisbah masu tabbatar da tarbiya a jihar Kano sun kama fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya
- An kama Murja ne bayan an shafe tsawon lokaci ana yi mata nasiha kan yada bidiyo na rashin tarbiya ba tare da ta ji ba
- Hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ibrahim, ne ya sanar da batun kamun nata a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano karkashin jagorancin, Sheikh Aminu Daurawa, ta kama fitacciyar jarumar nan mai amfani da manhajar TikTok, Murja Ibrahim Kunya.
Labarin kamun Murna na 'kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ibrahim, ya fitar a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @babarh_.
Me yasa aka kama Murja?
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa an kama jarumar ne bayan an sha yi mata nasiha ba tare da ta sauya halinta ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Murja dai tana cikin shahararrun 'yan Tiktok guda shida da hukumar ta Hisbah ta sanar da nemansu ruwa a jallo.
Ana dai zarginsu da furta kalaman rashin tarbiya a bidiyon da suke yadawa, wanda hakan ya saba dokar tabbatar da tarbiya.
Ba wannan bane karo na farko da hukumar ke zaunar da Murja domin yi mata nasiha don ganin ta zama mutuniyar kwarai wacce za a yi alfahari da ita a cikin al'umma.
A kan haka ne ma, aka rahoto a baya cewa hukumar Hisbah za ta aurar da 'yar TikTok din a watannin baya, sai dai kuma har yanzu ba a kai ga haka ba.
Hadimin gwamnan ya rubuta:
"Bayan nasiha da jan hankali, hukumar Hisbah a jihar Kano, ta kama fitacciyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya."
Jama'a sun yi martani bayan Hisbah ta kama Murya Kunya
@Mr_stranger442 ya yi martani:
"Don Allah a Barta a nan har sai tayi tsatsa.
"Wannan yarinyar da sauran irin ta ba qaramar annoba bane a cikin al’umma."
@KhnSyf92414 ya yi martani:
"Gaskiya yakamata wan nan dai ayi mata wani babban hukun cin saboda yan baya don Gaskiya abun nata yana wuce gona da iri."
Murja ta aikewa Hisbah da sako
A baya mun ji cewa Murja Kunya ta maida martani yayin da aka ji ana nemanta.
Murja Kunya a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Facebook tayi wa hukumar Hisbah raddi da cewa sun san inda ta ke.
Asali: Legit.ng