Sabuwar Baraka Ta Kunno Kai Yayin da Tsohuwar Hadimar Buhari ta Caccaki Tinubu, An Yi Karin Bayani
- Tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie, ta caccaki gwamnati mai ci ta Shugaban kasa Bola Tinubu
- Yayin da ake fama da tsadar rayuwa a kasar, Onochie ta zargi gwamnatin Tinubu da kin daurawa daga inda tsohon ubangidanta ya tsaya
- A shafinta na soshiyal midiya, ta tambayi inda shinkafa iri-iri da aka samar gwamnatinsu kamar su 'Lake Rike, Ebonyi Rice' da sauransu suka shiga
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Shugaban kasa Bola Tinubu ya sake shan caccaka saboda gazawar gwamnatinsa wajen ci gaba da manufofin magabacinsa, Muhammadu Buhari.
Lauretta Onochie, tsohuwar hadimar tsohon shugaban kasa Buhari kuma tsohuwar shugabar hukumar NDDC, ta garzaya shafinta na soshiyal midiya don tambayar inda shinkafar da ake yi a gwamnatin ubangidanta suka shiga.
Dalilin da yasa Onochie ta caccaki gwamnatin Tinubu
A wani rubutu da ta yi a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 'yar siyasar haifaffiyar Niger Delta, ta zargi gwamnati mai ci karkashin Tinubu da rashin ci gaba daga inda aka tsaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta tambayi abin da ya faru da shinkafar 'Lake Rice', shinkafar 'Ebonyi Rice' da wasu da dama bayan ta wallafa hotunansu a shafin nata.
Ta rubuta:
"Me ya sa muke guje wa ci gaba? Me ya faru da shinkafar 'Lake Rice', ' Ebonyi Rice', da dai sauransu?"
Yadda 'Lake Rice' ta yi battan dabo
Shinkafar 'Lake Rice' na daya daga cikin abubuwan da aka samar daga manufar habbaka noma ta gwamnatin Buhari. An samar da shi ne ta hanyar hadaka tsakanin gwamnatin Legas da Kebbi.
An fara samar da shinkafar a 2016 lokacin gwamnatin tsohon gwamna Akinwunmi Ambode na jihar Legas da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito, shinkafar ta bace sosai a lokacin kullen shekarar 2020 a Legas.
Shekaru biyu da fara ta, shinkafar ta bace a kasuwa bayan wata yarjejeniyar fahimtar juna ta noma da gwamnati ta sanya wa hannu. Ba a magance matsalar ba har sai da Ambode ya bar ofis a ranar 29 ga Mayu.
Ga wallafar Onochie:
Jigon APC ya magantu kan halin da ake ciki
A wani labarin, mun ji cewa duk wahalar da ake kukan ana sha a yau, Adams Oshiomhole yana ganin ba su da dangantaka da tsare-tsaren Bola Tinubu.
Adams Oshiomhole ya cire hannun gwamnatin Bola Tinubu daga kangi da tsadar rayuwa, ya ce duk laifin Muhammadu Buhari ne.
Channels ta rahoto Sanatan Arewacin jihar Edo a majalisar dattawa yana nunawa ‘yan Najeriya illar canza kudi da bankin CBN ya yi.
Asali: Legit.ng