Babbar Magana: Tsagerun Ƴan Bindiga Sun Kashe Fitaccen Lauyan Najeriya

Babbar Magana: Tsagerun Ƴan Bindiga Sun Kashe Fitaccen Lauyan Najeriya

  • Wasu ƴan bindiga da ba a sani ba sun halaka Barista Victor Onwubiko, a kan hanyarsa ta komawa jami'ar jihar Abia daga mahaifarsa da ke Imo
  • Rahotanni sun bayyana cewa lauyan ya rasa ransa ne ranar Asabar da daddare a kan titin Okigwe zuwa Oturu, wanda ake yawan kai hare-hare
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya sun nuna cewa miyagun ƴan bindiga sun halaka lauya masanin doka, Victor Onwubiko, ɗan asalin jihar Imo.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, lauyan da ƴan bindigan suka kashe yana zaune ne a Uturu da ke jihar Abiya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

Sufetan yan sanda na ƙasa, IGP Kayode.
Yan Bindiga Sun Halaƙa Fitaccen Lauyan Najeriya a Jihar Imo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Yadda maharan suka aikata ɗanyen aiki

Wata majiya ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Okigwe/Uturu tsakanin karfe 8 zuwa 9 na dare a ranar Asabar 10 ga watan Fabrairu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar, ƴan bindigan sun yi ajalin fitaccen lauyan yayin da suka kai farmakin satar mutane a kan titin da daddare.

Majiyar ta ce:

"Ƴan bindiga sun kashe lauyan wanda daga bisani aka gano sunansa, Barista Victor Onwubiko a kan titin Okigwe. Mamacin ɗan asalin garin Okigwe a jihar Imo ne amma yana rayuwa a jami'ar jihar Abia da ke Uturu."
"Yana kan hanyar komawa jihar Abia inda yake zaune kwatsam sai ‘yan bindiga suka yi masa kwanton bauna, suka kashe shi a titin Okigwe/Uturu."
"A ƴan kwanakin nan ana ta fama da hare-haren satar mutane a wannan titin duk da tulin jami'an tsaron da ke jibge a wurare daban-daban na titin."

Kara karanta wannan

Gwamnoni sama da 6 sun sa labule kan muhimmin abu 1 da ya shafi ƴan Najeriya, bayanai sun fito

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai ranar Litinin, Tribune ta tattaro.

A kalamansa, kakakin ƴan sandan ya ce:

"Muna aiki kan lamarin yanzu haka, nan ba da daɗewa ba zan fitar da sanarwa a hukumance."

Yan bindiga sun sace matafiya a Ondo

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun tare motar Bas mai ɗaukaar fasinja 18, sun kashe direba kana suka yi awon gaba da sauran gaba ɗaya a jihar Ondo.

Dakarun sojoji, ƴan sanda da wasu jami'an tsaro sun dira wurin da lamarin ya afku, sun kewaye dazukan yankin da nufin ceto matafiyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262