Yan Bindiga Sun Kashe Dan Takarar Majalisar Wakilai Na Jam’iyyar PDP
- Yan bindiga sun sace wani dan takarar majalisar wakilai tare da dan uwansa a jihar Anambra, daga bisani suka kashe shi
- An ruwaito cewa dan siyasar mai suna Mista Oguejiofor ya kasance yana yawan rubuce rubuce akan hare-haren 'yan bindigar
- A hannu daya kuma, mahaifin Mista Oguejiofor ya suma tare da shekawa barzahu bayan da ya samu labarin 'yan bindigar sun kashe ɗansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Anambra - Wasu ‘yan bindiga sun kashe tsohon dan takarar majalisar wakilai daga jihar Anambra, Jude Oguejiofor.
Mista Oguejiofor ya fito ne daga Orsumoghu da ke karamar hukumar Ihiala a Anambra amma yana zaune a Nnewi da ke karamar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar.
Mista Oguejiofor, wanda kuma lauya ne, ya tsaya takarar dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Ihiala a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da ya sa 'yan bindigar suka kashe Oguejiofor
Majiyoyi sun shaida wa Premium Times cewa wasu ‘yan bindiga sun sace dan siyasar ne da misalin karfe 1 na safe a makon jiya, tare da dan uwansa.
Lamarin ya faru ne a unguwar Orsumoghu inda suka je ganin iyayensu. Amma daga baya ‘yan bindigar sun sako dan uwansa ba tare da sun raunata shi ba.
Wata majiya na kusa da dangin da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wannan jaridar cewa ‘yan bindigar sun zargi Mista Oguejiofor da rubuta koke a kansu da ayyukansu a cikin garin.
'Mahaifin Oguejiofor ya mutu'
A halin da ake ciki, majiyar ta ce mahaifin Mista Oguejiofor ya suma kuma ya mutu a ranar Alhamis lokacin da ‘yan bindigar suka tuntubi iyalan suka sanar da su cewa sun kashe dan siyasar.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a ranar Litinin, ya shaida cewa ba shi da wani bayani kan lamarin.
Kamar sauran jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya, tsaro ya tabarbare a jihar Anambra, inda 'yan bindiga ke yawan kai hare-hare.
Yan bindiga sun kai sabon hari Nasarawa, sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kai sabon farmaki kauyen Umaisha a jihar Nasarawa.
A yayin harin ne kuma suka kashe sojoji uku tare da 'yan banga biyu da ke yawon sintiri don wanzar da zaman lafiya a yankin.
Rahotanni sun bayyana cewa an tura sojoji karamar hukumar Toto ne don kwantar da wata tarzoma da ake yi tsakanin wasu kauyuka biyu.
Asali: Legit.ng