Miyagun Ƴan Bindiga Sun Tare Matafiya, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar APC
- Yan bindiga sun tare motar Bas mai ɗaukaar fasinja 18, sun kashe direba kana suka yi awon gaba da sauran gaba ɗaya a jihar Ondo
- Dakarun sojoji, ƴan sanda da wasu jami'an tsaro sun dira wurin da lamarin ya afku, sun kewaye dazukan yankin da nufin ceto matafiyan
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tura ƙarin dakarun yaƙi da masu garkuwa domin ceto mutanen da kuma kama maharan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Wasu miyagun ƴan bindiga da ba a sani ba sun kwashe fasinjojin motar bas mai wurin zaman mutum 18 a jihar Ondo ranar Jumu'a da ta gabata.
Channels tv ta ce ƴan bindigan sun sace matafiyan a bodar garin Akunu-Akoko a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa da garin Ayere da ke ƙaramar hukumar Ijumu duk a jihar.
Masu garkuwa da mutanen sun kashe direban bas din tare da kwashe dukkan fasinjojin motar zuwa cikin wani daji da ke kusa, inda suka bar wata karamar yarinya a wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa matafiyan da ke bin titin ne suka gano motar bas ɗin a ajiye a gefen titi bayan ƴan bindigan sun kwashe mutanen ciki gaba ɗaya.
Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?
Jim kaɗan bayan haka ne jami'am tsaro da suka haɗa da sojoji, ƴan sanda, jami'an Amotekun da mafarautan yankin suka kai ɗauki wurin, inda suka mamayi dajin da ke kusa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, SP Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta rabawa ƴan jarida a Akure, babban birnin jihar.
Ta kuma bayyana cewa tuni kwamishinan ƴan sanda, Abayomi Oladipo, ya tura tawagar dakarun yaƙi da masu garkuwa zuwa yankin domin kubutar da waɗanda aka sace.
A halin yanzu dai rundunar ƴan sandan ta kewaye yankin baki daya a kokarin kubutar da wadanda lamarin ya shafa tare da cafke masu garkuwa da mutane, Tribune ta rahoto.
An sake kai sabon hari jihar Filato
A wani rahoton na daban Wasu mahara sun kashe akalla rayukan mutum huɗu a wasu sabbin hare-hare da suka kai ƙauyukan karamar hukumar Bassa a jihar Filato.
Mai magana da yawun rundunar sojin Operation Save Haven, Oya James, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sojoji ne suka kori miyagun.
Asali: Legit.ng