Tsadar Rayuwa: Sanatan Kano Ya Yi Magana Kan Matakan da Tinubu Ke Dauka, Ya Yi Alkawari a Bangarensa
- Yayin da ake cikin wani mawuyacin hali, Sanata Barau Jibrin ya yabawa Tinubu kan irin matakan da ya ke dauka kan haka
- Mataimakin shugaban Majalisar ya bukaci gwamnatocin jihohi da na Tarayya da su yi koyi da Tinubu wurin fitar da abinci
- Ya ce a bangarensa ya yi alkawarin bayar da shinkafa ga gidaje dubu 200 don saukakawa mutane mummunan halin da suke ciki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan halin kunci da ake ciki.
Sanata Barau ya ce wannan matsalar ba iya Najeriya kadai ba ce illa duk duniya ana fama da hauhawan farashin kaya.
Mene Barau ke cewa kan matakin Tinubu?
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barau ya yabawa Shugaba Tinubu kan fitar da tan dubu 102 na kayan abinci daga Baitul Mali don saukakawa mutane.
Yayin da ya ke yabon Tinubu, Sanatan ya ce wannan mataki zai taimaka matuka wurin rage wa jama’a radadin tsadar kayan.
Sanata Jibrin ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ismail Mudashir.
Wace bukata Barau ya tura ga jama’a?
Ya bukaci gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da su yi koyi da matakin Tinubu don taimakawa jama’a.
Wane alkawari Barau ya yi ga jama'a?
Ya yi alkawarin ba da gudunmawar shinkafa ga gidaje dubu 200 a kokarinsa na kawo dauki a halin da ake ciki.
A cewarsa:
“A wannan hali da ake ciki, ya kamata dukkanmu mu goyi bayan GwamnatinTarayya baya don dakile matsalar tsadar abinci.
“Mun sani cewa matsalar tsadan abinci ba iya Najeriya kadai ba ne illa duniya ce gaba daya.
“Daliln haka ne nake kira ga gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi da su yi koyi da Tinubu wurin raba kayan abinci ga mabukata.”
Kwankwaso ya yi magana kan matakin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa, jigon APC a jihar Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya yi magana kan halin da ake ciki.
Kwankwaso ya yabawa Shugaba Tinubu ganin irin matakan da ya ke dauka don ganin an dakile matsalar tare da saukakawa mutane.
Asali: Legit.ng