Zanga-Zanga Ta Barke a Abuja, Hotuna da Bidiyo Sun Bayyana
- Ma’aikatan jinya da unguwar zoma sun gudanar da zanga-zanga a Abuja don nuna rashin amincewa da sabbin ƙa’idojin tantance satifet da hukumar NMCN ta fito da su
- Ma’aikatan jinya sun ce sabbin dokokin wani yunƙuri ne na daƙile ƴancin da suke da shi na neman damarmaki idan sun samu
- Masu zanga-zangar sun buƙaci hujumar da ta magance matsalolin da suka shafi jin daɗinsu da suka haɗa da ƙarancin albashi, ƙarancin ma'aikata, da sauran haƙƙoƙinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ma’aikatan jinya a ƙarƙashin ƙungiyar ma’aikatan jinya da unguwar zoma ta ƙasa reshen Abuja, sun fara zanga-zanga.
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, zanga-zangar an gudanar da ita ne kan sabbin ƙa'idojin tantance satifiket da hukumar Nursing and Midwifery Council (NMCN) ta fitar.
Jaridar Vanguard ta ce zanga-zangar ta faru ne a ofishin NMCN da ke Abuja a ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairun 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma’aikatan jinya da unguwar zoman sun yi ta rera waƙoƙi da baje ɗaga alluna a kusa da harabar ginin hukumar.
Menene dalilin yin zanga-zangar?
Ma’aikatan jinya suna ƙorafi kan abin da suka bayyana a matsayin yunƙurin hana su ƴancin yin aiki.
Suna neman hukumar ta magance matsalolin jindaɗin ma'aikatan jinya, yanayin albashi, ƙarancin ma'aikata, da sauran haƙƙoƙinsu.
Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ke kan allunan na cewa:
"A magance rashin aikin yi tsakanin ma’aikatan jinya, a magance matsalar ma'aikatan jabu, a magance matsalar jin daɗin ma'aikatan jinya.
"#Ba mu yarda da sabbin ƙa'idodin tantancewa ba. A daina ba ma’aikatan jinya na Najeriya takaici, mun riga mun sha wahala sosai, a kare ma’aikatan jinya, a kare lafiya, NMCN, mun ce a’a ga ƙa’idojin tantancewa, NMCN, kar a rage ma’aikatan jinya" da sauransu.
Ga wasu hotuna da bidiyo ƙasa:
An Yi Zanga-Zanga a Legas
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu mutane a jihar Legas sun fito domin gudanar da zanga zanga kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Masu zanga-zangar waɗanɗa mata ne da matasa sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya ɗauki domin yunwa ta yi yawa a ƙasa.
Asali: Legit.ng