Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Wasu Tsageru Suka Kai Sabon Mummunan Hari a Jihar Arewa
- Wasu mahara sun kashe akalla rayukan mutum huɗu a wasu sabbin hare-hare da suka kai ƙauyukan karamar hukumar Bassa a jihar Filato
- Mai magana da yawun rundunar sojin Operation Save Haven, Oya James, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sojoji ne suka kori miyagun
- Ƙungiyar Irigwe IDA ta yi Allah wadai da harin kana ta ɗora laifin kan fulani makiyaya amma shugaban Fulani ya ƙaryata zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin da wasu miyagu suka kai sabon farmaki a kauyen Nkienzha da ke yankin Miango a ƙaramar hukumar Bassa, jihar Filato.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, bayan mutum uku da suka mutu a harin, ƙarin wasu mutum biyu sun samu raunuka daban-daban.
Mai magana da yawun rundunar sojojin Operation Safe Haven, Kaftin Oya James, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce ɗaukin da sojoji suka kai ne ya sa maharan suka tsere.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin kungiyar Irigwe (IDA), Davidson Malison, ya tabbatar da lamarin ranar Litinin, ya ce an kashe mutum uku ranar Lahadi, ɗaya kuma ranar Asabar da ta wuce.
Mutum nawa aka kashe a sabon harin Filato?
Ƙungiyar IDA ta zargi fulani makiyaya da kai wannan hari, wanda shugaban ƙungiyar fulani makiyaya (GAFDAN), Garba Abdullahi, ya fito ya musanta.
Malison ya bayyana sunayen wadanda aka kashe da suka haɗa da, Gadan Zhwe (50), Lydia Yakubu (48), Nuhu Yakubu (23), da Musa Wolo (32).
Channels tv ta rahoto Malison na cewa:
"Ƙungiyar ƴan kabilar Irigwe ta ƙasa ta hannun IDA ta yi tir da wannan harin, ta kuma bayyana shi a matsayin rashin imani da tausayi, kuma tana kira ga masu aikata hakan su shiga taitayinsu.
"Muna kira ga hukumomin tsaro su damƙo dukkan masu hannu a wannan lamari domin su girbi abinda suka shuka a gaban doka kuma muna kira da a dawo mana da zaman lafiya a yankinmu."
Tun da farko ranar Juma’a aka kashe wani makiyayi mai suna Abas Sani, mai shekaru 16 a duniya a lokacin da yake kiwo a ƙauyen Teegbe da ke karamar hukumar Bassa.
Sojoji sun ceto mutane 18
A wani rahoton na daban Dakarun rundunar sojin Najeriya sun kai samame mafakar ƴan bindiga a Katsina, sun ceto mata 18 da aka yi garkuwa da su.
Kwamandan rundunar Birgade ta 17 ya ce sojojin sun yi gumurzu da ƴan ta'addan kafin su samu wannan nasara.
Asali: Legit.ng