Gwamna Ya Sanar da Duniya, ‘Yan Bindiga Na Shirin Kawo Masa Hari a Arewacin Najeriya
- Dikko Umar Radda ya ce shi karon kan shi bai tsira daga harin da ‘yan bindiga su ke shiryawa ba
- Mai girma gwamnan ya sanar da wannan a lokacin da ya kebe da wasu manya a gidan gwamnati
- Gwamnan Katsina ya bukaci mutanensa su tashi tsaye su kare kan su daga ta’adin ‘yan bindiga
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Katsina - Mai girma Dikko Umar Radda, ya shaida cewa ya na cikin mutanen da ‘yan bindiga su ke neman kawowa hari a halin yanzu.
Gwamnan jihar Katsina ya bayyana wannan ne a lokacin da ya yi zama da masu ruwa da tsaki kamar yadda Channels ta rahoto.
'Yan bindiga sun fitini Katsina
Gwamna Dikko Umar Radda ya kira taron tsaro na gaggawa a gidan gwamnati a makon jiya domin magance matsalolin Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai girma Dikko Radda ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun fito da wata sabuwar dabara ta yin garkuwa da talakawan da ke wahala.
Gwamna ya ce 'yan bindiga sun rasa 'Informa'
Rahoto ya ce abin da ya faru kuwa shi ne masu taimaka masu da bayanai ba su nan.
Gwamna Radda yake cewa a yanzu miyagun sun fara hada-kai da sauran ‘yan ta’addan da ke wasu jihohi domin sace mutane.
Duk da kokarin da gwamnan na Katsina yake yi a fannin tsaro, ya ce ‘yan bindiga sun dage sai an dawo da hannun agogo baya.
A wajen wannan zama ne gwamna Radda ya yi kira ga al’ummarsa su kare kan su, sannan ya yi batun matsananciyar tsadar rayuwa.
Za a kai wa Gwamna Dikko Radda hari?
Bayanan sirrin tsaro da gwamnan ya samu ya nuna yana cikin wadanda ake so a kai masu hari, kuma ya ce hakan bai dame shi ba.
Aminiya ta rahoto Gwamnan yana cewa barazanar ba za ta hana shi da gwamnatinsa tabbatar da zaman lafiya a Katsina ba.
Amma idan dai ba a tashi tsaye ba, Dikko Radda ya koka da cewa ‘yan ta’addan da suka addabi Katsinawa za su ga bayan jihar.
'Yan bindiga sun dauke mutane
Rahoton da aka samu kwanakin baya ya nuna 'an bindiga sun sace mutum 16 a wani sabon hari da aka kai a akyen Kogo a Katsina.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani mummunan hari a kauyen Kogo da ke karamar hukumar Faskari.
Asali: Legit.ng