An Ba Tsohon Gwamnan APC Muhimmiyar Shawara Kan Binciken Badakalar N80bn da EFCC Ke Yi Masa

An Ba Tsohon Gwamnan APC Muhimmiyar Shawara Kan Binciken Badakalar N80bn da EFCC Ke Yi Masa

  • Ƙungiyar matasan Arewa (NEYGA) ta zargi tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello da yiwa hukumar EFCC ƙazafi
  • NEYGA ta buƙaci Bello da ya yarda ya miƙa kansa domin gudanar da bincike a kansa bisa zargin N80bn
  • Kungiyar ta ce Yahaya Bello bai fi sauran tsofaffin gwamnonin jihohin da hukumar EFCC ke bincike a kansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wata kungiya mai suna Northern Ethnic Youth Group Assembly (NEYGA), ta ce ya kamata tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya wanke kansa gaban hukumar EFCC bisa zarginsa da hannu a badaƙalar naira biliyan 80.

NEYGA ta roƙi Bello da ya daina ƙoƙarin ɓata sunan hukumar EFCC, da yin kamar ya fi ƙarfin doka.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta shiga sabuwar matsala kan tuhumar tsohon gwamna, bayanai sun fito

An ba Yahaya Bello shawara
An bukaci Yahaya Bello ya kai kansa gaban EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello, EFCC
Asali: Facebook

Kakakin ƙungiyar, Ibrahim Dan-Musa ya bayyana haka a wata sanarwa da Legit.ng ta samu a ranar Juma’a, 9 ga watan Fabrairun 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi NEYGA ta yi kan Yahaya Bello?

Dan-Musa ya ce yunƙurin Bello na ɓata sunan EFCC da shugabanta wani yunƙuri ne na karkatar da hankali kan zargin da ake yi masa.

Ƙungiyar ta buƙaci Bello da ya miƙa kansa domin bincike tare da amsa tambayoyin da suka dace domin wanke sunansa daga zarge-zargen da ake yi masa na zamba.

Ya kuma yi Allah-wadai da yadda Bello ya maƙale a gidan gwamnatin jihar Kogi domin kaucewa bincike.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“Yahaya Bello bai wuce tsofaffin gwamnoni irinsu Fayose, Jolly Nyame, Dariye, Ramallan Yaro, da sauran waɗanda ake bincike a kansu ba.
"Duk ɗan Najeriya ya san cewa Bello ya yi amfani da dukiyar ƙasa ba bisa ƙa'ida ba, kuma dama a ƙarshe rana irin wannan za ta zo."

Kara karanta wannan

An bayyana masu hannu a zargin daukar nauyin ta'addanci da ake yi wa Sanatan Arewa

An Kai Ƙorafin EFCC Kan Binciken Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan Kogi mazauna ƙasashen waje (KIDA), ta shigar da ƙorafi kan hukumar EFCC kan binciken tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Ƙungiyar ta buƙaci ofisoshin diflomasiyya da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da su gaggauta shiga tsakani ta hanyar amfani da tasirinsu, domin daƙile abin da suka kira ƙoƙarin ɓata sunan tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng