Bidiyon ‘Dan Majalisar Kano Yana Rutsa Gwamnan CBN Kan Maida Ofisoshi Zuwa Legas

Bidiyon ‘Dan Majalisar Kano Yana Rutsa Gwamnan CBN Kan Maida Ofisoshi Zuwa Legas

  • Aliyu Sani Madakin-Gini shi ne wakilin mazabar Dala da ke jihar Kano a majalisar wakilan tarayya
  • ‘Yan majalisa sun gayyaci Gwamnan CBN ya yi masu karin haske a kan halin da tattali ya shiga
  • Madakin-Gini ya nemi jin dalilin dauke wasu sassan CBN daga babban birnin Abuja zuwa Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A makon nan majalisa ta gayyaci gwamnan bankin CBN, Yemi Cordoso domin ya yi bayani game da halin da tattali yake ciki.

Aliyu Madakin-Gini yana cikin wadanda suka jefa tambayoyi ga Yemi Cordoso kamar yadda bidiyon da ya daura a Facebook ya nuna.

Gwamnan CBN
Gwamnan CBN a Majalisa Hoto: @Cenbank/Aliyu Sani Madaki
Asali: Twitter

CBN ya dauke ofisoshi daga Abuja

‘Dan majalisar ya nemi jin dalilin dauke wasu ofisoshi daga hedikwatar bankin wadanda a tsawon shekaru 20, a Abuja aka san su.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta titsiye gwamnan babban banki CBN kan muhimmin batu, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Madakin-Gini ya nemi jin ko akwai burbushin siyasa da kabilanci a janye wadannan ofisoshi zuwa Legas kamar yadda ake ta zargi.

‘Dan siyasar ya ce karin hasken ya zama dole ne ganin yadda lamarin ya jawo surutu.

Baya ga haka, ‘dan majalisar na NNPP ya koka kan yadda rayuwa tayi tsada, ya nemi jin kokarin da CBN yake yi kan karyewar Naira.

Maganar 'dan majalisa a kan Gwamnan CBN

Aliyu Madaki ya rubuta a shafinsa:

“Tambayoyi da nayi wa Gwamnan banki na kasa a kan dauke wasu units/deparment na bankin kasa da kuma karyewar naira."

- Aliyu Madaki

Ya kara da cewa:

“Daga karshe dai babu wata cikakkiyar amsa daga gare shi.”

- Aliyu Madaki

Da ya tashi amsa tambayoyin, Cordoso ya karyata zargin da ake yi wa CBN da gwamnatin Bola Tinubu na yunkurin karya wani bangare.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran APC ya fallasa komai, ‘yan siyasa na amfani da addini domin mulkin Filato

Martanin Gwamnan CBN, Yemi Cordoso

"Babu wani zancen ziyasa ko kadan, bankin CBN yana da rassa a duka jihohi 36 da ke kasar nan."
"Akwai bukatar daidaita karfinmu da arzikinmu tsakanin bangarori musamman inda ake samun bayanai."
"Ko a kasar Amurka haka abin yake, mu na so mu daidaita kwarewarmu ne kurum."

- Aliyu Madaki

Meyasa jami'an CBN suka koma Legas?

A bidiyon, an ji gwamnan babban bankin ya na nanata cewa barin Abuja zai rage kashe kudi, za a rage hawa jirgin sama zuwa Legas.

Cordoso ya bada misali da sashen kula da bankuna, yake cewa ya kamata ma’aikatan bangaren su koma kusa da hedikwatocin bankuna.

Aikin gama ya gama a CBN

Kwanaki aka ji an dauke ma’aikatan CBN musamman a bangarorin kula da bankuna, tsare-tsaren tattali da biyan kudi daga Abuja.

Sabon gwamna Yemi Cardoso ya dage kan batun rage jami’an da ke Abuja daga 4, 200 zuwa 3, 700 saboda wasu dalilai da ya kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng