'Yan Sanda Sun Bi Hatsabibin Mai Garkuwa Mabuyarsa Sun Sheke Shi Da 'Yaransa' a Abuja
- 'Yan sanda a babban birnin tarayya Abuja sun yi nasarar halaka wani hatsabibin shugaban masu garkuwa da mutane Musa Wada Magaji wanda aka fi sani da Sabo
- Tawagar 'yan sandan na musamman sun bi sahun masu garkuwan ne a mabuyarsu da ke tsaunin Mpape inda suka yi musayar wuta na misalin mintuna 30 kafin samun galaba a kan miyagun
- Mai magana da yawun 'yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da hakan yana mai cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba sai ta ga bayan miyagun da ke neman tayar da zaune tsaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abuja - Jami'an yan sandan Najeriya sashen masu bincike na musamman sun kashe hatsabiban masu garkuwa da mutane, ciki harda gawurtaccen nan Musa Wada (Sabo) Magaji a wani sumame suka kai a Mpape, a Abuja.
Rukunin sun kuma lalata sansanonin masu garkuwar wanda suka addabi mazauna Abuja a yan kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu garkuwar, cikin wata sanarwa ranar Asabar ta hannun mai magana da yawun rundunar yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi sun farmaki 'yan sanda da bindigu wanda aka yi bata kashi tsawon mintuna 30, wanda ya yi sanadiyar munanan raunika yayin da daya daga cikin jami'an harsashi ya same shi.
Ya ce:
"An samu wannan nasarar ganin bayan Abubakar Wada, abokin aikin Musa Wada, ranar 8 ga watan Fabrairun 2024, wanda ke matsayin shugaban tawagarsu.
"Musa Wada da aka fi sani da Sabo, shi ke kitsa mafi yawancin garkuwar da ake yi a yankin Mpape da Bwari a Abuja; Kagarko a Kaduna; Masaka, da kauyen Nukun a Jihar Nasarawa.
"Ya na bin salon gano masu kudi tare da shirya tawagar garkuwa da kuma tawagar karbo kudin fansa."
Ya cigaba da cewa:
"An yi nasarar wargaza maboyarsu da ke bayan tsaunukan Mpape, wanda jami'an tsaro na musamman suka gudanar cikin salo na musamman wanda ya janyo nasarar kawar da hatsabiban yan ta'addar."
Abubuwan da aka kwato daga masu garkuwa?
"Bayan haka, an gano wayoyin salula da tarin layuka, layu, miyagun kwayoyi, wanda ke a matsayin manyan hujjoji don taimakawa bincike. Ana ci gaba da kokarin gano makamai da harsashi da sauran kayan aikin da suke gudanar da miyagun ayyukan.
"Rundunar yan sanda na cigaba da bakin kokari don kawar da bata gari da wanzar da kwanciyar hankali da zaman lafiya ga 'yan kasa, kuma za ta ci gaba da daukan matakai don kawo karshen ayyukan ta'addanci da kuma hukunta masu aikata laifukan ta kowanne hali."
Asali: Legit.ng