'Yan Fansho Sunyi Barazanar Yin Zanga-Zanga Zigidir, Sun Bayyana Dalili
- Tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci na cigaba da adabar 'yan Najeriya daga bangarori daban-daban tun bayan cire tallafin man fetur
- Kungiyar 'yan fansho na Najeriya ta nuna rashin jin dadinta bisa mawuyacin halin da mambobinta ke ciki ta kuma nemi a kara fansho mafi karanci zuwa N100,000
- Mr Godwin Abumusi, shugaban kungiyar 'yan fansho na Najeriya ya yi barazanar cewa 'yan kungiyarsa za su fita titi suyi zanga-zanga zigidir idan gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba
Abuja - Kungiyar 'yan fansho na Najeriya ta ce mambobinta za su fita titi su yi zanga-zanga zigidir idan ba a inganta walwalarsu ba cikin dan kankanin lokaci a kasar.
Shugaban kungiyar na kasa, Godwin Abumusi, ya fada wa 'yan jarida a Abuja a ranar Juma'a cewa kungiyarsa za ta dauki wannan matakin don janyo hankalin duniya kan halin da 'yan fansho ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Zan jagoranci 'yan fanshon Najeriya.
"Ina nufin, za mu fita zanga-zanga zigidir a tituna, don duniya ta ga 'yan fanshon Najeriya suna zanga-zanga tsirara.
"Idan suna so, su kama mu su ce, 'Me yasa kuka fita titi ba tufafi?."
Wane hali 'yan fansho ke ciki?
Jinkiri wurin biyan 'yan fansho ba sabon abu bane a Najeriya kuma 'yan fansho sun saba zanga-zanga. Mista Abumusi ya ce ba halin da 'yan fansho ke ciki yana da wahalar fahimta.
Ya koka da cewa:
"A Najeriya, gwamnati ba ta tunanin talakawa. Kansu kawai suke tunani. Idan ba haka ba, ta yaya za a rika biyan 'yan fansho har N450 a Enugu. Ta yaya haka zai kasance."
A yayin da rayuwa ke kara tsada kuma kungiyoyin kwadago ke neman sabon albashi mafi karanci, 'yan fansho suma suna neman a sake duba batun fansho mafi karanci.
Mene 'yan fanshon Najeriya ke bukata daga gwamnati?
Mr Abumusi ya bayyana abin da 'yan fansho ke bukata domin su iya rayuwa a tattalin arziki na yanzu.
Ya ce:
"Muna son kwamitin albashi su ajiye N100,000 a matsayin fansho mafi karanci a kasar yayin da kungiyar kwadago ke neman N200,000 a matsayin albashi mafi karanci; duk wani abu da ba haka ba zai janyo fushin 'yan fansho da ke fama da matsin tattalin arziki."
Asali: Legit.ng