'Yan Sanda Sun Cafke Babban Malamin Addini Kan Safarar Kananan Yara, Bayanai Sun Fito

'Yan Sanda Sun Cafke Babban Malamin Addini Kan Safarar Kananan Yara, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja ta samu nasarar cafke wani fasto bisa zargin yin safarar ƙananan yara
  • Kakakin rundunar ƴan sandan birnin, Josephine Adeh, ta ce an cafke faston ne tare da wasu mutum biyu lokacin da suke safarar yaran
  • Ta bayyana cewa yaran waɗanda su 12 ne an yi safararsu ne zuwa jihar Ogun lokacin da ƴan sanda suka tare motar da ke ɗauke da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami’an rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun cafke wani fasto bisa zargin safarar ƙananan yara.

Jami'an na tawagar RRS 74, sun cafke faston ne mai suna Simon Kado, ɗan uwansa, Jesse Simon-Kado, da direbansu, Muhammad Isah, bisa zargin yin safarar yara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Arewa, sun sace gomman mutane

'Yan sanda sun cafke fasto
'Yan sanda sun cafke fasto kan zargin safarar kananan yara a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

An kama su ne a ranar Juma’a yayin da suke safarar yara ƙanana 12, da suka haɗa da mata takwas da maza hudu ƴan shekara biyar zuwa 16 daga jihar Nasarawa zuwa jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, 10 ga watan Fabrairu.

Ta yaya ƴan sanda suka cafke su?

Adeh ta ce jami'an ƴan sandan na RRS 74 sun tare motar ne ƙirar Toyota Hiace mai ɗauke da lamba APP 489 XE, a ranar Juma'a da misalin ƙarfe 12:55 na dare.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Binciken farko ya nuna cewa yaran da shekarunsu ke tsakanin shekara 15 zuwa shekara 16, dukkansu daga ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa, ana safararsu ne zuwa jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 12 da ya kamata su sanni kan wasan Ƙarshe da Najeriya zata fafata da Ivory Coast

"Binciken ya nuna cewa wani Fasto Simon Kado da wani Jesse Simon-Kado, wanda a halin yanzu suna hannun ƴan sanda ne su ke safarar yaran zuwa jihar Ogun."

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Shugaban Ƴan Bindiga a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa, jami'an rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja, sun samu nasarar sheƙe wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga.

Jami'an ƴan sandan sun sheƙe ɗan bindigan ne a wani samame da suka kai kan maɓoyarsa da ke wajen birnin na Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng