An kama wata mata yar shekara 45 da ke safarar yara tare da yara 23 a Taraba

An kama wata mata yar shekara 45 da ke safarar yara tare da yara 23 a Taraba

- Jami'an yan sanda sun kama wata mai safarar yara, Mary Yakubu, tare da yara 23 a jahar Taraba

- Yaran wadanda ke a tsakanin shekaru hudu da bakwai sun hada da maza 14 da mata tara

- An tattaro cewa an kama mai laifin ne tare da yaran a wani garejin mota a karamar hukumar Bali da ke jahar yayinda suke shirin shiga mota

Rundunar yan sanda ta kama wata mai safarar yara, Mary Yakubu, tare da yara 23 a jahar Taraba.

Yaran wadanda ke a tsakanin shekaru hudu da bakwai sun hada da maza 14 da mata tara.

An gurfanar da Mary ne tare da wasu masu laifi a ranar Litinin, 2 ga watan Fabrairu a hedkwatar rundunar yan sanda da ke jahar a Jalingo, babbar birnin jahar Taraba.

Kakakin rundunar yan sandan jahar, David Misal, ya fada ma manema labarai cewa an kama mai laifin ne tare da yaran a wani garejin mota a karamar hukumar Bali da ke jahar yayinda suke shirin shiga mota.

Ya bayyana cewa an mika yaran guda 23 zuwa ga ma’aikatar kula da jin dadin jama’a a jahar.

An kama wata mata yar shekara 45 da ke safarar yara tare da yara 23 a Taraba
An kama wata mata yar shekara 45 da ke safarar yara tare da yara 23 a Taraba
Asali: UGC

Misal ya kara da cewa an kama iyayen wasu daga cikin yaran su bakwai wadanda ke da nasaba da laifin yayinda ake bincike don kama sauran.

A nata bangaren, mai laifin ya yi ikirarin cewa iyayan yaran ne suka bata su domin ya baiwa wadanda ke bukatar yara don su kula masu da su.

“Iyayen yaran sun nemi na zo na sama masu mutanen da za su taimaka masu da daukar dawainiyar karatunsu saboda a kauyen babu makarantu.

“Wannan shine karo na farko da nake aikata hakan, ban karbi kowani kudi daga hannun iyayensu ba,” in ji Mary.

Ya Kara da cewa “ji uwar yara bakwai ne kuma malamar makaranta a makarantar firamare na Adamu da ke karamar hukumr Bali. Ni yar shekara 45 ce kuma an kama ni ne a garejin mota a Bali lokacin da nake shirin tafiya da yaran.”

KU KARANTA KUMA: Suleiman Yusuf: Mai gadin gidan radiyon da ya zama minista

Kakakin yan sandan ya kuma gurfanar da wasu masu garkuwa da mutane su bakwai da ke addabar mutane a yankunan jahar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel