Shugaba Tinubu Ya Taso Daga Abuja Domin Halartar Wani Muhimmin Taro a Jihar Arewa
- Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga birnin tarayya Abuja ya kama hanyar zuwa Kaduna domin halartar bikin cikar makarantar sojoji shekara 60
- Ofishin mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin midiya ne ya tabbatar da haka a wata gajeruwar sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Asabar
- Makarantar sojojin ta shafe mako guda tana gudanar da bukukuwan cika shekara 60 da kafauwa, Tinubu zai halarci tarom rufewa yau Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya baro babban birnin tarayya Abuja da safiyar ranar Asabar ɗin nan, inda ya nufi jihar Kaduna.
Shugaba Tinubu ya kamo hanyar zuwa Kaduna domin halartar bikin cika shekaru 60 na makarantar horar da dakarun sojoji (NDA) da ke jihar Kaduna.
Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokun midiya, D. Olusegun, shi ne ya tabbatar da haka a wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a manhajar X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya fitar da safiyar yau Asabar, 10 ga watan Fabrairu, 2024, hadimin shugaban ƙasar ya ce:
"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar birnin Abuja domin halartar taron makarantar Sojoji NDA da ke Kaduna."
Ranar 5 ga watan Fabrairu, 2024 makarantar ta kaddamar da babbar alamar da ke nuna ta cika shekara 60 duk a wani ɓangare na bukukuwan da ta shirya wanda ke gudana a Afaka.
Wadanda suka halarci wurin sun haɗa da sojojin da aka yaye a NDA, tsoffin kwamandoji, hafsoshin soja masu aiki da masu ritaya, jami’an sauran kungiyoyi da hukumomin tsaro.
Yaushe Bola Tinubu zai koma Abuja
Ana sa ran Tinubu zai koma Abuja a wannan rana kuma da yiwuwar zai wuce zuwa Abidjan, babban birnin Ivory Coast.
Zai je ƙasar ne domin kallon fafatawa tsakanin Najeriya da Côte d’Ivoire a wasan ƙarshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka AFCON.
APC ta tantance ƴan takara 12 a Edo
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta tantance ƴan takarar gwamna 12 da zasu fafata a zaben fidda gwani a jihar Edo.
Kwamitin tantance yan takarar jihar Edo ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren tsare-tsaren APC ta ƙasa.
Asali: Legit.ng