Bayan Sace 'Yan Kai Amarya, 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Mutane a Jihar Arewa
- 'Yan bindiga sun sake kai hari kauyen Kogo da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a daren Alhamis, 8 ga watan Fabrairu
- Maharan sun yi garkuwa da mutane 16 da suka hada da kananan yara, mata da kuma maza zuwa inda ba a sani ba
- An rahoto cewa sun kai harin ne a tsanaki bayan sun ajiye baburansu daga bakin hanya don gudun kada a gano su
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki kauyen Kogo a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da mutum 16 ciki harda yara, mata da maza.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wani mazaunin yankin ya bayyana cewa harin, wanda aka kai a sirrince da misalin karfe 8:20 na daren Alhamis ya zo wa mutanen kauyen a bazata.
Ya bayyana cewa maharan sun aiwatar da shirin nasu ne cikin tsanaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"'Yan bindigan sun kutsa garin cikin nutsuwa, suna masu ajiye baburansu daga nesa don gudun kada a gano su.
“Ba tare da hayaniya ba, maharan suka nufi wani gida inda daga karshe suka tafi da mutane 16 da suka hada da yara, mata da maza."
A yanzu dai ana zaman dar-dar da rashin tabbass a garin, inda ake jiran karin haske kan lamarin da ke gudana.
Wata majiya ta bayyana cewa mazauna yankin sun shiga damuwa matuka game da lafiyar 'yan uwansu da aka sace da ma tsaron yankin baki daya.
Me hukumar 'yan sanda ta ce?
Da aka tuntune shi, kakakin 'yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa zai tabbatar da rahoton da yin karin bayani.
Sai dai har zuwa lokacin kawo wannan rahoton, babu wani karin bayani ko tabbaci daga wajensa, rahoton Daily Post.
Gwamnan Katsina ya kira taron gaggawa
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya kira taron gaggawa na majalisar tsaro ranar Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024.
Gwamna Raɗɗa ya kira wannan taro cikin gaggawa ne domin lalubo hanyoyin magance tsadar rayuwar da ake fuskanta da kuma rashin tsaro a jihar Katsina.
Asali: Legit.ng