Tashin Hankali Yayin Da Direban Motar Bas Ya Cinnawa Mai Bada Hannu a Titi Wuta
- Wani direban motar bas ya cinnawa wani jami'in hukumar EDSTMA mai kula da zirga-zirgan ababen hawa a jihar Edo wuta
- An rahoto cewa direban ya aiwatar da hakan ne bayan an umurci jami'in mai bada hannu a titin da ya kai motar direban ofishin su
- Yanzu haka jami'in na hukumar EDSTMA yana jinya a wani asibiti da ke garin Benin yayin da direban ya ci na kare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Benin, Jihar Edo - Wani direban motar bas ya cinnawa jami'in hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa na jihar Edo wuta.
Mummunan al'amarin ya afku ne bayan direban ya keta danjar bada hannu da ke mararrabar Adesuwa hanyar Sapele a ranar Juma'a, 9 ga watan Fabrairu.
Yadda direban mota ya babbaka mai bayar da hannu a titi
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, an umurci jami'in na EDTSMA da ya dauki motar direban zuwa ofishin su bayan ya ki yarda a kama shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa direban motar ya tsere bayan ya yi aika-aikar yayin da jami'in ke jinya a wani asibiti da ke garin Benin, babban birnin jihar.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, wani jami'in hukumar EDSTMA da ya tabbatar da faruwar lamarin a bidiyo a soshiyal midiya ya ce:
"Direban ya aikata laifin tuki, sannan jami'an Zone 2 suka kama shi sannan suka bukace shi da ya dauki motar zuwa sansaninsu amma ya ki, ya hana a kama shi sannan ya fara fada da kowa."
Ya ci gaba da cewa:
"Yanzu haka da muke magana jami'in na samun kulawa a wani asibiti a nan Benin. Direban motar bas din ya tsere."
Matasa sun kona gidan basarake
A wani labarin, mun ji cewa an samu tashin hankali a yankin Ojah, karamar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo.
Lamarin ya faru ne bayan wasu fusatattun matasa a garin sun kai farmaki tare da cinnawa fadar Olojah na Ojah, Oba Okogbe Lawani wuta a ranar Talata, 30 ga watan Janairu.
Asali: Legit.ng