AFCON: Shehu Sani Ya Bai Wa Mata Hanyoyin Kare Mazajensu Daga Mutuwa Yayin Kallon Kwallo
- Sanata Shehu Sani ya ba da wasu muhimman shawarwari ga mata musamman wadanda mazajensu ke kallon kwallo
- Sani ya ba da shawarwarin ne yayin da ake dakon wasan karshe tsakanin tawagar Super Eagles da kasar Ivory Coast
- Wannan na zuwa ne bayan wasu ‘yan Najeriya guda biyar sun rasa ransu yayin wasan Najeriya da kasar Afirka ta Kudu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna – Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya bai wa mata shawara don kare mazajensu daga mutuwa yayin kallon kwallo.
Sani ya shawarci matan da su kula sosai da mazajensu musamman wadanda suka san masoya harkon kwallon kafa ne.
Wasu shawarwari Shehu Sani ya bayar?
Wannan shawari na Sanatan na zuwa ne yayin da wasu ‘yan Najeriya biyar suka rasa ransu yayin wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Faburairu yayin bugun fenareti inda Najeriya ta yi nasarar tsallakewa zuwa wasan karshe.
Sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na X a yau Juma’a 9 ga watan Faburairu inda ya ba da hanyoyin kare faruwar hakan.
A cewarsa:
“Idan har kinsan mijinki masoyin kallon kafa ne musamman a talabijin kuma kina kokwanton lafiyarsa akwai matsala.
“Ki je ki kashe wutar gidan gaba daya kuma kada ki manta kisan hanyar da zaki bi don lalata janareta saboda kada ya kalli wasan.”
Yadda 'yan Najeriya suka mutu kan wasan
Mutuwar wadannan ‘yan Najeriya ya tayar wa mutanen kasar hankali duk da nasarar da Super Eagles ta samu a wasan.
Daga cikin wadanda suka mutum akwai jigon APC kuma tsohon dan Majalisar Tarayya da kuma mataimakin Bursar a Jami’ar Kwara.
Sauran sun hada da matashi mai bautar kasa daga Kaduna da wani jigon dan kasuwa a jihar Anambra sai kuma wani magidanci daga jihar Ogun.
Tawagar Super Eagles ta yi addu’a
Kun ji cewa tawagar kungiyar Super Eagles ta yi addu’a ga wadanda suka rasa ransu yayin wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.
Kyaftin din tawagar, Ahmed Musa shi ya jagoranci addu’ar inda ya yi alkawarin dawo da kofin gida saboda wadanda suka mutu da ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng