Majalisar Dattawa Ta Titsiye Gwamnan Babban Banki CBN Kan Muhimmin Batu, Bayanai Sun Fito
- Majalisar dattawa ta hannun kwamitin harkokin kudi ta fara zaman sauraron ƙarin haske daga gwamnan babban bankin ƙasa CBN
- Kwamitin ya gayyaci gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya bayyana a gabansa domin yin bayani kan halin da tattalin arziƙin Najeriya ke ciki a yanzu
- Wannan mataki ya zo yayin da darajar Naira ke ci gaba da faɗuwa a kasuwar canji lamarin da ya haddasa tsadar rayuwa ga ƴan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawa kan harkokin kudi, banki, inshora da cibiyoyin hada-hadar kuɗi ya fara zaman titsiye tawagar da ke kula da tattalin arzikin ƙasa.
Tawagar dai ta ƙunshi wasu manyan jagororin babban bankin Najeriya ƙarƙashin jagorancin gwamnan CBN, Yemi Cardoso, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Bayanai sun nuna cewa Cardoso ya jagoranci tawagar CBN zuwa gaban kwamitin domin amsa tambayoyi yau Jumu'a, 9 ga watan Fabrairu, 2024, Vanguard ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa majalisar dattawa ta gayyaci gwamnan CBN?
A ranar 31 ga watan Janairu ne kwamitin na majalisar dattawa ya gayyaci gwamnan babban bankin kasar domin ya bayyana a gabansa kan muhimman batutuwa.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake nuna damuwa kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki da kuma faduwar darajar Naira a kasuwar canji.
Sanatocin sun bukaci babban bankin kasar CBN ya yi musu ƙarin haske kan dimbin kalubalen tattalin arziki da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
Sanata Adetokunbo Abiru ya jaddada bukatar gudanar da binciken kwakwaf game da hada-hadar kuɗaɗen da aka yi a baya da kuma yanayin ɗa'ar bankin.
Duba da yadda talauci da rashin tsaro ke cin kasuwa a sassan ƙasar nan wanda ya haufar da ƙarancin abinci, majalisar na ganin CBN ba zai iya bugun ƙirji ya ce tsarukansa na aiki ba.
Amma Sanata Orji Kalu ya ƙara da cewa dole ne gwamnati ta koma ta daina amfani da dala wajen hada-hadar kasuwanci, inda ya koka kan raguwar FDI a kasar nan.
Majalisar wakilai ta ɗauki mataki
A wnai rahoton kuma Majalisar wakilai ta yi magana kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran wahalhalun da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.
Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ya ce shi da sauran ƴan majalisa suna shan radadi irin wanda al'umma ke sha a yanzu.
Asali: Legit.ng