Hedikwatar Tsaro Ta Fadi Abu 1 da Za a Yi Don Kawo Karshen Matsalar Rashin Tsaro a Najeriya
- Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta yi magana kann hanyar da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a ƙasar nan
- DHQ ta bayyana cewa idan ana son ganin an kawar da matsalar tsaron, dole ne ƴan Najeriya su zama masu kishin ƙasarsu
- Ta bayyana cewa dakarun sojoji za su ci gaba da na su ƙoƙarin domin ganin an samu zaman lafiya a ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana hanyar da za a bi domin magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan.
DHQ ta bayyana cewa idan har ana son ganin ƙarshen matsalar, dole ne ƴan ƙasar nan su kasance masu kishin ƙasarsu, cewar rahoton The Nation.
Ta ce yaƙi da ta'addanci da masu tayar da ƙayar baya na buƙatar haɗin kan kowa da kowa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DHQ ta bayyana hakan ne ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Manjo Janar Edward Buba, yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu.
Sojoji za su ci gaba da ragargazar ƴan ta'adda
Buba ya ce sojoji za su ci gaba da gudanar da aikinsu na farauta da lalata ƴan ta’adda a faɗin ƙasar nan ta hanyar da ta dace., rahoton Vanguard ya tabbatar.
A kalamansa:
"Ba sai an faɗa ba, waɗannan ƴan ta’adda suna da zaɓi biyu ne kawai, wato ko dai a kashe su ko su miƙa wuya.
"Burin mu shine mu maido da zaman lafiya da tsaro domin ƴan kasa su samu rayuwa mai dadi. Za mu ci gaba da yin hakan duk da halin da ake ciki.
"Sojoji za su ci gaba da fafatawa da gagarumin ƙoƙari, da azama, da sadaukarwa don samar da sakamako mai kyau.
"Muna kira ga dukkan ɓangarorin al’umma da su yi koyi da jajirtattun sojojin mu a fagen yaƙi da ke faɗa don cimma burin fatattakar ƴan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasar nan domin dawo da zaman lafiya da tsaro.
"Waɗannan sojojin maza da mata, sun fito ne daga kowane lungu da sako na ƙasarmu, kuma suna aiki kafada da kafada a matsayin rundunar ɗaya, don cimma manufar ruguza sansanonin tashe-tashen hankula a ƙasar nan."
Sojoji Sun Ceto Mutum 18 a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mata 18 da ƴan ta'adda suka sace a jihar Katsina.
Dakarun sojojin sun ceto mutanen ne a wani samame da suka kai a maɓoyar ƴan ta'addan da ke dazukan Yan Tumaki da Dan Ali na jihar.
Asali: Legit.ng