Jimami Yayin da Fitacciyar Jarumar Fina-finai Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, an Fadi Dalilin Ajalinta
- An shiga wani irin yanayi bayan rasuwar fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe a jihar Legas da ke kudancin Najeriya
- Marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu a jihar Legas bayan ta sha fama da cutar daji na tsawon lokaci
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan tace fina-finai, Dakta Shaibu Husseini ya fitar a daren jiya Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe ta riga mu gidan gaskiya, kamar yadda TheCable ta tattaro.
Marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu a Legas bayan ta sha fama da cutar daji na tsawon lokaci.
Yaushe marigayiyar ta rasu?
Jarumar kafin rasuwarta a Legas ta fito a fina-finai da dama wanda ta ba da gudunmawa sosai wurin ilmantarwa da fadakarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban Daraktan tace fina-finai, Dakta Shaibu Husseini shi ya bayyana haka a daren jiya Laraba 7 ga watan Faburairu, cewar Daily Post.
A cewarsa:
"Na samu labarin rasuwar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe a yau Laraba 7 ga watan Faburairu."
"Jarumar wacce daga bisani ta dawo Fasto ta mutu ne bayan fama da cutar daji a jihar Legas."
Dan jarida ya riga mu gidan gaskiya
"Tabbas za mu yi rashinta musamman iyalina wanda musamman muka saka sunan 'yar mu a matsayin takwararta, ubangiji ya jikanta."
Har ila yau, a jiya ne masoya harkokin wasanni a Najeriya suka shiga makoki yayin da wani fitaccen dan jaridan wasanni, Kayode Tijani ya rasu.
Marigayin ya rasu ne jiya Laraba a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas bayan ya sha fama da jinya.
Jarumi Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya
Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya a jihar Ogun.
Solanke ya rasu ne a ranar Talata 6 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da doguwar jinya.
Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 81 a duniya inda ya ce ga garinku bayan daukarsa zuwa asibiti.
Asali: Legit.ng