Majalisar Osun Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, an Gano Dalili

Majalisar Osun Ta Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, an Gano Dalili

  • Majalisar dokokin jihar Osun ta dakatar da shugaban karamar hukumar Ede ta Kudu saboda kama shi da laifin rashin da'a
  • An ruwaito cewa shugaban karamar hukumar, Mr. Afolabi ya furta kalaman cin mutunci ga kakakin majalisar jihar a wajen wani taro
  • Mambobin majalisar ne suka saka hannu a takardar dakatar da Afolabi tare da nada mataimakinsa matsayin shugaban Ede

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Osun - A ranar Laraba, majalisar dokokin jihar Osun ta dakatar da shugaban karamar hukumar Ede ta Kudu, Mr. Lukman Afolabi.

Dakatarwar ta biyo bayan musayar baki da aka samu tsakanin Afolabi da kakin majalisar jihar, Hon. Adewale Egbedun a wajen wani taro.

Kara karanta wannan

Gwamnan CBN da ministocin Tinubu 2 sun bayyana a gaban majalisa, sun yi bayanai masu muhimmanci

Yan majalisar Osun sun fusata kan yadda Afolabi ya zagi kakakin majalisar.
Yan majalisar Osun sun fusata kan yadda Afolabi ya zagi kakakin majalisar. Hoto: @AOEgbedun
Asali: Twitter

Abun da ya faru tsakanin Mr. Afolabi da kakin majalisar

Binciken Tribune Online ya nuna cewa a yayin da suke musayar bakin ne Afolabi ya furta kalaman cin mutunci ga dan majalisar, lamarin da ya fusata Egbedun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har yanzu dai ba a gano abin da ya kai ga faruwar lamarin ba, sai dai an iya gano cewa kakin majalisar ya fita daga dakin taron zuwa ofishin sa.

Wasu daga cikin mambobin majalisar jihar da lamarin ya bata wa rai, sun tattauna a tsakaninsu tare da neman a dakatar da shugaban karamar hukumar.

Majalisar ta fitar da sanarwar dakatar da Mr. Afolabi

A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na kakakin majalisar, Olamide Tiamiyu, 'yan majalisun sun tsige Afolabi nan take, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da saurayi ya gutsire kan budurwarsa a Bayelsa

A cewar sanarwar:

"Majalisar jihar Osun ta dakatar da shugaban karamar hukumar Ede ta Kudu, Mr. Lukman Afolabi, saboda aikata rashin da'a.
"An kuma umurci dakataccen shugaban karamar hukumar da ya mika dukkanin wasu abubuwa na gudanar da mulki zuwa ga mataimakinsa."

Majalisa ta fara yi wa kudin tsarin mulki garambawul

A wani labarin kuma, majalisar tarayya ta ce nan da ƙarshen shekarar 2025 za ta kammala bitar kundin tsarin mulkin Najeriya don yi masa gyare-gyare.

Mataimakin kakakin majalisar, Mista Benjamin Kalu ya ce an kafa kwamiti da zai yi wa kundin kwaskwarima wanda ake sa ran zai shafi ci gaban 'yan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel