Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dan Takarar Gwamnan PDP da Aka Gurfanar Gaban Kotu

Kotu Ta Dauki Mataki Kan Dan Takarar Gwamnan PDP da Aka Gurfanar Gaban Kotu

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Ladi Adebutu, ya shiga cikin matsala
  • Adebutu da wasu mutum biyar na fuskantar tuhuma a gaban kotu kan zargin sayan ƙuri'u a lokacin zaɓen gwamnan jihar
  • Sai dai kotun ta bayar da belin ɗan takarar kan N1m bayan lauyansa ya buƙaci hakan tare da ɗage sauraron ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - A ranar Talata gwamnatin tarayya ta gurfanar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jihar Ogun a zaɓen 2023, Oladipupo Adebutu, a gaban kotu.

An gurfanar da Adebutu ne bisa tuhume-tuhume bakwai, da suka shafi batun sayen ƙuri’u da sauran laifukan zaɓe a zaɓen gwamnan da aka yi ranar 18 ga watan Maris, 2023, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta nuna bajinta, ta samu gagarumar nasara

Kotu ta ba da belin Adebutu
Adebutu ya yi takarar gwamnan jihar Ogun a 2023 Hoto: Adebutu Campaign Organisation
Asali: Facebook

Meyasa aka gurfanar da Adebutu?

An gurfanar da Adebutu ne tare da wasu mutum biyar a gaban mai shari’a Abiodun Akinyemi na babbar kotun jihar Ogun dake kan titin Kobape, a Abeokuta, rahoton Channels tv ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanda ake tuhumar, sun ƙi amsa laifukan da ake tuhumar su da su a cikin ƙarar mai lamba AB/10c/2023.

Tun da farko a shari’ar, lauya mai shigar da ƙara na gwamnatin tarayya, Rotimi Jacobs (SAN), ya shaida wa kotun cewa an yi wa tuhume-tuhumen waɗanda ake ƙara kwaskwarima.

Ya nemi ya maye gurbin tsohuwar tuhumar da sabuwa, buƙatar da kotun ta amince da ita tun da lauyan waɗanda ake ƙara, Gordy Uche (SAN) bai nuna adawa da hakan ba.

Bayan gabatar da shari'ar, Uche ya roƙi kotun da ta amince ta bayar da belin Adebutu saboda ƙimarsa, inda ya ce shi da kansa ya kawo kansa gaban kotun kuma ba zai gudu ba.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan halaka mutum 17 a wani sabon hari a jihar Arewa

Sai dai mai gabatar da ƙara ya ce duk da cewa ba ya adawa da neman belin, bai kamata ya kasance saboda ƙimarsa za a bayar ba.

Alkali ya yi hukunci

A hukuncin da ya yanke, mai shari’a Akinyemi ya bayar da belin Adebutu a kan N1m tare da mutum ɗaya da zai tsaya masa.

Alƙalin ya ce wanda zai tsaya masa na iya kasancewa dan uwa ne ko kuma wani na kusa da shi.

An ɗage sauraren ƙarar har zuwa yau Laraba domin fara shari’ar.

EFCC Ta Yi Caraf da Kanin Minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta cafke ƙanin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika.

Hukumar EFCC ta cafke ƙanin ministan ne bisa zargin karkatar da N8bn na ma'aikatar sufurin jiragen saman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng