Damfarar N3m: Alkali Ya Ci Tarar ‘N20’ Maimakon Aika Mai Laifi Kurkukun Shekaru 3

Damfarar N3m: Alkali Ya Ci Tarar ‘N20’ Maimakon Aika Mai Laifi Kurkukun Shekaru 3

  • An samu wata mata mai suna Rose Dogara Silas Gyar da laifin damfarar wani Bawan Allah kudi
  • Matar ta hada kai da Mohammad Babayo Maina, aka karbe N3m hannun Saifullahi Sani Abdullahi
  • Wanda aka damfara ya kai maganar EFCC, alkali ya yanke Rose Gyar hukuncin dauri a gidan gyara hali

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Gombe - An yanke wani hukunci wanda ya ba mutane mamaki a wani babban kotun jihar Gombe a karkashin mai shari’a Abdul Hamid.

Jaridar PM News ta ce Alkali Abdul Hamid ya umarci Rose Dogara Silas Gyar ta biya N20 domin ta kauracewa zaman gidan gyaran hali.

EFCC, N20
EFCC v Rose Dogara Silas Gyar Hoto: Getty Images, EFCC
Asali: Getty Images

A shari’ar da EFCC mai yaki da rashin gaskiya tayi da Rose Dogara Silas Gyar, an samu matar da laifin cin N3m ta haramtaciyyar hanya.

Kara karanta wannan

Sanata ya fadakar da mutane a kan hanyoyi 3 da za a bi domin karya Dalar Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Madam Rose Dogara Silas Gyar ta damfari wani Saifullahi Sani Abdullahi kudi har N3m da karyar za ta nemo masa bashin kaya a CBN.

Akwai tsarin bada aron kudi da babban bankin kasar ya kawo domin masu noma.

Dogara Gyar da wani Mohammad Babayo Maina sun yaudari Saifullahi Sani Abdullahi cewa zai samu kayan gona daga bankin CBN.

Nairaland ta ce lauyan EFCC ya yi karar Gyar da Babayo Maina bisa zargin damafara domin sun nemi N3m, wannan abin ya faru ne tun 2021.s

Asiri ya tonu da EFCC ta je kotu

A karshe dai Saifullahi Sani Abdullahi ya kai wadannan mutane kara gaban hukuma domin ya tashi babu kayan noma kuma babu kudinsa.

Ana shiga kotu, wanda ake kara ta amsa laifin cin N3,000,000.00 don haka lauyan masu kara, M.D Aliyu ya ce Alkali ya yanke hukunci.

Kara karanta wannan

Adadin kujerun APC a Majalisa ya bayyana da surukin tsohon Sanata ya zama Sanata

Tarar N20 ko N20, 000?

EFCC ta kawo labarin a shafinta, amma ta ce N20, 000 aka nemi Rose Dogara Silas Gyar ta biya ko dai tayi shekaru uku a gidan gyaran hali.

S.O Kumu wanda yake kare matar ya roki kotu tayi mata rangwame domin ganin Gyar tayi nadama, kuma ta maida duk kudin da ta karba.

EFCC v Yahaya Bello

Dazu aka samu labari sabon Gwamnan Kogi, Ahmed Ododo ya yi martani kan zargin da ake yi wa Yahaya Bello na satar kudin jihar a mulki.

Mai girma Ahmed Ododo ya ce wasu 'yan siyasa ne suka dauki nauyin EFCC domin ganin sun bata wa tsohon gwamnan jihar suna a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng