Kano: Jami’ar Dangote Ta Dauki Mataki Kan Wani Lakcara da Aka Gano a Bidiyo Ya Na Hukunta Dalibai
- Hukumar gudanarwa ta Jami'ar jihar Kano ta dakatar da wani lakcara bayan ya ci zarafin dalibai a cikin aji
- An gano lakcaran a wani faifan bidiyo ya na hukunta daliban kamar a makarantun firamare da sakandare
- Lauya mazaunin Kano, Abba Hikima a cikin wata budaddiyar wasika ya yi Allah wadai da wannan mataki na lakcaran
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku
Jihar Kano - Hukumar Jami'ar jihar Kano da ke Wudil ta dauki mataki kan wani lakcara da ya hukunta dalibai.
Jami'ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha ta dauki matakin dakatar da lakcaran ne bayan cin zarafin daliban a cikin aji.
Mene ake zargin lakcaran da aikatawa?
An gano lakcaran a wani faifan bidiyo ya na hukunta daliban kamar a makarantun firamare da sakandare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lakcaran ya saka su tsugunawa kan gwiwowinsu kafin daga bisani da saka su tsallen kwado a cikin dakin karatun.
Malamin ya dauki wannan matakin lokacin da ya ke koyar da daliban darasin "Mutanen Najeriya da Al'adunsu", cewar Leadership.
Daga bisani bayan tsallen kwadon an gano shi ya na marin wani daga cikin dalibai a cikin ajin.
Martanin lauya Abba Hikima a Kano
Lauya mazaunin Kano, Abba Hikima a cikin wata budaddiyar wasika ya yi Allah wadai da wannan mataki na lakcaran.
Dakatar da lakcara na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami'ar ta fitar a jiya Talata 6 ga watan Faburairu.
Hukumar makaranta ta tura dakatataccen lakcaran zuwa kwamitin ladabtarwa don daukar mataki.
Ta kuma ba da tabbaci ga iyaye da sauran al'umma cewa ta himmatu wurin tabbatar da kare lafiyar yaransu.
Ta kara da cewa za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau don koyar da dalibai yadda ya kamata.
An bukaci Majalisa a Kano ta mayar da Sunusi
Kun ji cewa wata kungiya a jihar Kano ta tura wasika zuwa Majalisa kan sake duba dokar masarautun jihar.
Kungiyar 'Yan Dangwalen Jihar Kano" ita ta tura wasikar inda ta bukaci a mayar da tsohon Sarkin Kano, Sunusi Lamido.
Asali: Legit.ng