'Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Shugaban 'Yan Bindiga, Bayanai Sun Fito

'Yan Sanda Sun Sheke Kasurgumin Shugaban 'Yan Bindiga, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta sanar da samun nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga a Abuja
  • Kakakin rundunar ƴan sandan, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa
  • Kakakin ya ya kuma ƙara da cewa an raunata sauran ƴan bindiga da dama a samamen da ƴan sandan suka kai maɓoyarsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jami’an rundunar ƴan sandan Najeriya sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Isa Dei-Dei a Abuja.

Jami'an ƴan sandan sun halaka ɗan bindigan ne bayan sun kai farmaki a maɓoyar ƴan bindiga da ke wajen birnin tarayya Abuja.

An kashe dan bindiga a Abuja
'Yan sanda sun halaka kasurgumin dan bindiga a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

An ce jami’an ƴan sandan da ke aiki da sashen leƙen asiri na rundunar ƴan sandan ne suka gudanar da aikin.

Kara karanta wannan

Hukumomin tsaro sun fadi sabbin bayanai kan sanatan Arewa da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Yadda aka kashe ɗan bindigan

Adejobi ya yi nuni cewa yayin da Dei-Dei kawai aka kashe, an harbi wasu daga cikin ƴan bindigan da suka tsere yayin fafatawar, inda suka samu raunukan harbin bindiga.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Da misalin ƙarfe 10:15 na safiyar ranar 5 ga watan Fabrairun 2024, jami’an DFI-IRT da ke aikin leƙen asiri, sun samu bayanai kan maɓoyar wata ƙungiyar ƴan bindiga da wani Isa Dei-Dei ke jagoranta a wajen birnin Abuja, nan da nan suka zarce zuwa wurin da nufin yin kame.
"Da suka kusa zuwa wajen, su (ƴan bindigan) sun hango ƴan sandan sai suka gudu. Nan take ƴan sandan suka bi su, lamarin da ya kai ga musayar wuta mai zafi. A cikin musayar wutan, an kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isa Dei-Dei, yayin da wasu mambobin kungiyar suka yi nasarar tserewa da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke rikakken dan bindiga a Kano, bayanai sun fito

"Don haka muna kira ga jama’a musamman ma’aikatan lafiya da su sanar da mu kan duk wanda aka gani da raunin harbin bindiga domin ci gaba da bincike.”

Ƴan Sanda Sun Sace Mazaunin Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu gurɓatattun jami'an ƴan sanda sun yi garkuwa da wani ɗan kasuwa a birnin tarayya Abuja.

Jami'an ƴan sandan waɗanda tuni aka cafke su ana zarginsu da ƙwatar N29.9m daga hannun ɗan kasuwan da ƙarfin tsiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng