Tirkashi: An Kama Wani ‘Fatalwa’ Dan Shekara 59 a Adamawa
- Rundunar ‘yan sanda a Adamawa sun kama wani mutum dake yaudarar mutane da sunan Fatalwa
- Muhammad Abubakar mai shekaru 49 ya kware wajen damfarar mutane ta hanyar yi masu muryoyi iri-iri da sunan Fatalwa
- Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Nguroje ya ce sun kama Abubakar ne bayan ya damfari Abba Bale N300,000
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta sanar da kama wani mutum mai shekaru 49, Muhammad Abubakar kan yi wa Fatalwa sojan gona domin ya damfari jama'ar gari.
Abubakar, wanda ake zargin dan damfara ne, ya yi amfani da wannan dabara wajen damfarar wasu mutane da dama.
Ya yi ikirarin cewa ya shahara wajen kalmasa harshensa ta yadda yake iya yin zantuka da muryoyi iri-iri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kama Muhammad Abubakar
A cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, an garkame shi a ranar 5 ga watan Fabrairu bayan ya damfari wani mutum mai suna Abba Bale N300,000.
Nguroje ya ce:
"Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta kama wani mutum mai shekaru 59 dake yawan damfarar jama'a a ranar 5 ga watan Fabrairun 2024.
"Wanda ake zargin Muhammad Abubakar, wanda aka fi sani da Malam Sabo ya yi kaurin suna wajen damfara inda ya shahara wajen damfarar jama'a ta hanyar badda kama.
"Yawanci, yana boye ko shi wanene, sai ya yi karyan shi Fatalwa ne, tana mai magana da mutanen da kaidinsa ya ritsa da su da muryoyi daban-daban.
"Wanda ake zargin, ya kan canja murya wasu lokuta ya koma tamkar mace ko kananan yara yana mai damfarar mutane.
"A kwanan nan ya yaudari wani Abba Bale na Demsawo tare da damfararsa kudi naira dubu dari uku (300,000)."
'Yan sanda sun kama rikakken 'dan bindiga
A wani labarin, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kama wani ɗan bindiga mai suna Isah Lawal mai shekara 33, wanda ya fito daga yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Jaridar Leadership ta ce Lawal wanda ya ƙware a harkar fashi da makami, garkuwa da mutane, da satar shanu, an kama shi ne a wani samame da jami’an ƴan sanda ƙarƙashin jagorancin SP Aliyu Mohammed Auwal suka gudanar a jihar Kano.
Asali: Legit.ng