AFCON 2023: Shugaban Matasan APC Ya Shirya Babbar Liyafa Don Karfafa Guiwar Super Eagles a Abuja

AFCON 2023: Shugaban Matasan APC Ya Shirya Babbar Liyafa Don Karfafa Guiwar Super Eagles a Abuja

  • Shugaban jam'iyyar APC ya shirya wata kwarya kwaryar liyafa yayin da za a buga wasan kusa da na karshe tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu
  • An gani cewa za a fara taron liyafar ne misalin karfe 4 na yamma yayin da kuma za a take wasan da karfe 6 na yamma
  • Dayo Israel ya ce kofa a bude take ga duk wani dan Najeriya musamman matashi ya halarci liyafar a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban matasan jam’iyyar APC, Dayo Israel, ya shirya wata kwarya-kwaryar liyafa a sakatariyar jam'iyyar na Abuja domin karfafan guiwar ‘yan wasan Super Eagles.

Super Eagles za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da ke gudana a kasar Cote d’Ivoire.

Kara karanta wannan

Aikin gama ya gama: Dan takarar PDP ya sha kaye a zaben cike gurbi a Yobe, an fadi wanda ya lashe

Dayo Israel ya shirya liyafar karfafa guiwar tawagar Najeriya.
AFCON: Dayo Israel ya shirya liyafar karfafa guiwar tawagar Najeriya. Hoto: @dayoisrael
Asali: Twitter

Manufar hada wannan liyafar - Dayo Israel

A shirye shiryen wannan liyafar, Israel ya sayo wata saniya mai rai tare da yi mata ado da kalolin Najeriya da na tutar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Liyafar kallon kwallon a cewarsa, za ta hada kan matasan jam’iyyar APC da wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba a Abuja domin marawa tawagar Najeriya baya.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Isreal ya bayyana cewa za a gudanar da liyafar ne daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 6 na yamma.

Israel ya fadi abubuwan da za ayi a wajen liyafar

Ya rubuta cewa:

"Ku zo mu hadu a liyafa ta musamman tare da kallon wasan kusa da na karshe a gasar #AFCON2024 wanda shugaban matasan jam'iyyar APC ya shirya.

Kara karanta wannan

'Za a gwabza': Mai tsare ragar tawagar Afrika ta Kudu ta shirya karawa da Super Eagles a gasar AFCON

"Muna gayyatar kowa da kowa musamman matasa zuwa sakatariyar jam'iyyar na kasa da ke Abuja, inda za a fara goge wuya da karfe 4 na yamma gabanin take wasa."

Shugaban jam'iyyar ya ce an tanadi nau'ikan lemuka da kayan makulashe da suka hada da tsire da sauransu.

Israel ya kuma wallafa bidiyon sanuwar da za a yanka domin gudanar da liyafar yayin da ake kallon kwallon.

Kalli bidiyon a kasa:

AFCON: Hanyoyi 3 da Super Eagles za ta doke Afrika ta Kudu

A wani labarin kuma, an ba tawagar Super Eagles ta Najeriya shawarar hanyoyin da za ta bi don samun nasara akan tawagar Bafana Bafana ta Afrika da Kudu.

Daga cikin shawarwarin akwai tabbatar da cewa Super Eagles ta yi nasara cikin mintuna 90 ba sai an je zagayen buga finareti ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.