Jam'iyyar APC Ta Zargi Gwamnan PDP da Salwantar da N144bn, Ta Kawo Hujja
- Jam'iyyar APC a jihar Rivers ta zargi gwamnan jihar da salwantar da maƙudan kuɗaɗen da suka kai N144bn
- Shugaban riƙo na jam'iyyar a jihar, Tony Okocha, wanda ya yi zargin ya ce gwamnan ya karɓi kuɗaɗen ne daga asusun tarayya
- Okocha ya koka da cewa duk da karɓar waɗannan kuɗaɗen babu wata alamar cewa an yi jama'ar jihar aiki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Jam’iyyar APC reshen jihar Rivers ta zargi gwamnatin Gwamna Siminalayi Fubara da yin almubazzaranci da kuɗaɗen jihar.
Jam'iyyar dai ta yi zargin cewa gwamnan ya salwantar da maƙudan kuɗaɗen da suka kai har Naira biliyan 144.28 da ya karɓa daga asusun tarayya, cewar rahoton Leadership.
Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC a jihar, Cif Tony Okocha, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Port Harcourt, babban birnin jihar, yayin da yake magana a ziyarar da shugabannin jam’iyyar suka kai wa ƴan majalisar dokokin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'N144bn ta yi ɓatan dabo a Rivers' - APC
Okocha ya bayyana cewa, a bisa bayanan da jam’iyyar ta samu daga kwamitin raba asusun kuɗaɗen ajiya na tarayya (FAAC), gwamnatin jihar ta samu kuɗaɗen ne tsakanin watan Yunin 2023 zuwa watan Disamban 2023.
Ya bayyana takaicinsa da cewa kuɗaɗen waɗanda ba su cikin N10bn na kuɗaɗen shiga da ake samu a cikin gida, ba a yi amfani da su ba ta hanyar kawo ci gaba a jihar.
Shugaban kwamitin riƙon na jam’iyyar APC ya yi gargaɗin cewa jam’iyyar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani ɗan jam’iyyar da aka samu da hannu a almubazzaranci da dukiyar al’ummar jihar.
Da yake mayar da martani, kaƙakin majalisar dokokin jihar Rivers, Hon. Martins Amaewhule, ya godewa shugabannin jam’iyyar APC bisa wannan ziyarar, inda ya ce za ta ƙarfafa gwiwar ƴan majalisar.
Amaewhule ya ce
"Shawarar da kuka yi na ziyartar mu a nan za ta ƙarfafa mu. Majalisar dokokin jihar Rivers na alfahari da ku. Mu 27 muna jam’iyyar APC kuma muna farin cikin kasancewa a APC."
Gwamna Fubara Na Cikin Damuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya bayyana cewa yana cikin damuwa.
Gwamnan ya bayyana cewa ya shiga cikin damuwar ne sakamakon rikicin siyasar jihar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Asali: Legit.ng