Gwamnan Arewa Ya Kori Shugabannin Manyan Makarantun Jiharsa, Ya Ba Su Sabon Umarni
- Gwamnatin jihar Plateau ta sanar da korar shugaban jami'ar jihar da ke Bokkos daga kan muƙaminsa
- Gwamnatin ta kuma kori wasu shugabannin manyan makarantu huɗu na jihar daga kan muƙamansu
- Sakataren gwamnatin jihar wanda ya tabbatar da korar su a cikin wata sanarwa ya umarce su da su miƙa duk wata kadarar gwamnati da ke hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - An kori shugaban jami’ar jihar Plateau, Farfesa Bernard Matau daga muƙaminsa.
An naɗa Matau a matsayin shugaban jami’ar ne lokacin da yake riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar a gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamna Simon Lalong, cewar rahoton The Punch.
An tattaro cewa an kori shugaban jami’ar ne wanda wa’adinsa bai ƙare ba daga mukaminsa tare da wasu shugabannin manyan makarantun jihar guda huɗu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugabannin manyan makarantu a Plateau sun rasa muƙamansu
Shugabannin sun haɗa da na kwalejin fasaha ta jihar Plateau, Barkin Ladi, kwalejin fasaha ta lafiya, Pankshin, kwalejin fasaha ta lafiya, Zawan da kwalejin ilmi da ke Gindiri.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Samuel Jatau ya fitar ta tabbatar da korar a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairun 2024, rahoton Naijanews ya tabbatar.
Sanarwar ta ƙara da cewa
"Mai girma gwamnan Jihar Plateau, Barista Caleb Mutfwang ya amince da rusa majalisar gudanarwar jami’ar jihar Plateau da ke Bokkos nan take.
"Hakazalika, gwamnan ya kuma amince da korar shugabannin manyan makarantu kamar haka: Jami’ar jihar Plateau, Bokkos, kwalejin fasaha ta jihar Plateau, Barkin Ladi, Kwalejin Ilimi, Gindiri, kwalejin fasaha ta lafiya, Zawan da kwalejin fasaha ta lafiya, Pankshin."
Meyasa aka kore su?
Sanarwar wacce ba ta bayar da dalilin korar su ba, ta ce duk shugabannin da abin ya shafa su miƙa duk wata kadarar gwamnati da ke hannunsu ga manyan jami’ai mafi girma a makarantun.
Ya ƙara da cewa:
"Gwamnan ya kuma amince da soke ɗaukar ma’aikata da manyan makarantu suka yi tun a shekarar 2022 da farkon 2023 waɗanda aka dakatar."
Za a Sa Musulmai a Kwamitin Tsaro a Plateau
A ba ya rahoto ya zo cewa gwamnatin jihar Plateau ta yi alƙawarin sanya musulmai a cikin kwamitin tsaro da ta kafa a jihar.
Gwamnatin ta yi wannan alƙawarin ne bayan sukar da ta sha na ƙin sanya ko musulmi mutum ɗaya a kwamitin mai ɗauke da mutum 10.
Asali: Legit.ng