Gwamnan CBN da Ministocin Tinubu 2 Sun Gurfana Gaban Majalisa, Sun Yi Bayanai Masu Muhimmanci
- Gwamnan babban bankin Najeriya da ministocin Tinubu guda biyu sun bayyana gaban majalisar wakilan tarayya ranar Talata
- Majalisar ta gayyace su ne kan halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki da kuma faɗuwar darajar Naira
- Da yake jawabi, Cardoso ya bayyana matakan da CBN ke ɗauka da kuma hanyar da za a bi wajen tada komaɗar Naira
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya, Olayemi Cardoso, ya bayyana a gaban majalisar wakilai, inda ya yi jawabi kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Gwamnan CBN ya gurfana gaban mambobin majalisar ne yayin zamansu na yau Talata a birnin tarayya Abuja.
Cardoso ya yi musu bayani kan faduwar darajar Naira da sauran batutuwan da suka shafi harkar hada-hadar kudi na tattalin arzikin ƙasar nan, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun gayyace shi ne tare da ministan kudi kuma ministan da ke kula da tattalin arziki, Wale Edun da Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Atiku Bagudu.
Tun da farko, 'yan majalisar wakilan sun nuna matuƙar damuwa game da yadda takardun kuɗin Najeriya watau Naira ke ci gaba da faduwa kan dala.
Wane jawabi gwamnan CBN ya yi a majalisar?
Da yake ƙarin haske ga ƴan majalisar, Mista Cardoso ya ce ya zama tilas tattalin arziƙi ya riƙa samun tagomashi daga safarar kayayyaki zuwa kasashen waje wanda zai ɗaga darajar Naira.
Ya kuma ƙara da cewa CBN na kokarin samar da ƙwarin guiwa da aminci ta hanyar daidaita farashin kayan masarufi da kuma kasuwar ƴan canji.
Ya nuna yaƙinin cewa ana sa ran matakan da babban bankin ya ɗauka za su yi tasiri sosai kan hauhawar farashin kayayyaki.
A nasa jawabin, ministan kudin ya ce Najeriya na cikin yanayi mai kyau a fannin tattalin arziki fiye da yadda ta kasance a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Edun ya ce kasar ta kama hanyar faɗawa haɗari kafin shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya hau kan karagar mulki, amma ya aminta cewa an samu hauhawar tsadar rayuwa.
Da yake tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da kokarin agazawa mutane, ministan ya ce an maida hankali wajen inganta wutar lantarki domin jawo masu zuba hannun jari.
APC ta kara gurgunta APC a Jigawa
A wani rahoton kuma Tsohon shugaban matasa kuma ɗan a mutun Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a Jigawa.
Audu Mahmood ya taka muhimmiyar rawa a zaben 2023 a gundumar Garun Gabas da ke ƙaramar hukumar Mallam Madori.
Asali: Legit.ng