Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Tsohon Babban Hafsan Sojoji da Ake Zargi da Sace 21bn
- Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan ƙarar da ake tuhumar tsohon hafsan sojin NAF, Adesola Amosun, da wawure N21.5bn
- Hukumar yaƙi da rashawa EFCC ce ta gurfanar Amosun tare da wasu mutum biyu bisa tuhumar halasta kuɗin haram
- Sai dai da yake yanke hukunci yau Talata, Alkalin kotun ya ce kotu ba ta da hurumi saboda waɗanda ake kara suna kan aiki a wancan lokaci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta wanke tsohon babbana hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Adesola Amosun, da wasu mutum daga zargin karkatar da N21.5bn.
Kotun ta yi watsi da tuhumar halasta kuɗin haram da hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta shigar kan tsohon hafsan sojin da wasu mutum biyu, Punch ta ruwaito.
Yadda EFCC ta gurfanar da su a gaban ƙuliya
A watan Yuni, 2016, EFCC ta gurfanar da Amosun tare da tsohon akantan NAF, Air Vice Marshal Jacob Adigun da tsohon daraktan kuɗi da kasafi, Air Commodore Gbadebo Olugbenga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar ta gurfanar da su a gaban ƙuliya kan tuhume-tuhume 26 da suka shafi wawure kuɗin baitul malin rundunar sojin NAF.
Amma an sake gurfanar da su a gaban mai shari’a Chukwujekwu Aneke a kan tuhume-tuhume 13 da aka gyara a ƙara mai lamba FHC/L/280C/16 kan karkatar da kudaden da suka kai N21.5bn.
An gurfanar da wadanda ake tuhumar ne bisa zargin hada baki da kuma karkatar da kudaden na NAF zuwa aljihunansu, rahoton Premium Times.
Wane hukunci kotu ta yanke?
Da yake yanke hukunci kan bukatar waɗanda ake ƙara na a soke tuhumar da ake musu, mai shari'a Aneke ya amince da roƙon su.
Lauyan waɗanda ake tuhuma ya yi musun cewa kotun soji ce kaɗai ke da hurumin sauraron karar saboda a lokacin suna bakin aiki.
Alkalin ya amince da bayanin cewa kotun ba ta da hurumin sauraron wannan ƙara saboda a lokacin waɗanda ake zargi suna aiki a matsayinsu na sojoji.
Mai shari'a Aneke ya yanke cewa, "A matsayinsu na jami'an soji, ya kamata a fara bincikarsu a hannun sojojin tare da yi musu shari'a maimakon a gurfanar da su gaban kotun."
Ya ayyana binciken Amosun na ranar 30 ga watan Janairu, 2015, a matsayin mara amfani kana ya kuma soke tuhume-tuhumen da aka yi wa wadanda ake zargi.
Kotu ta hana belin magoya bayan Gwamna Fubara
A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan buƙatar belin magoya bayan Gwamna Fubara na jihar Ribas kan tuhumar ta'addanci.
Mutanen 5 da aka kama na fuskantar shari'a kan tuhume-tuhume bakwai da suka samo asali daga ƙona wani sashin majalisar dokokin Ribas.
Asali: Legit.ng