An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Shahararren Jarumin Fina-Finai a Najeriya da Shekaru 81
- An shiga jimami bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke wanda ya riga mu gidan gaskiya
- Marigayin ya rasu ne a yau Litinin 5 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci
- Dan Majalisar jihar da ke wakiltar Remo da Arewa, Hon. Dickson Awolaja ya tabbatar da mutuwar marigayin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun – Shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 81 a duniya.
Marigayin ya rasu ne a yau Litinin 5 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Yaushe marigayin ya rasu a jihar Ogun?
Channels TV ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu yayin da aka dauke shi daga kauyensu a karamar hukumar Remo zuwa asibiti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da rasuwarshi a asibitin koyarwa na Jami’ar Babcock da ke Ilesan a jihar Ogun
Marigayin ya sha fama da jinya inda aka tabbatar ya yi ta kai kawo daga gida zuwa asibiti tun a watan Disambar 2023.
Dan Majalisar jihar da ke wakiltar Remo da Arewa, Hon. Dickson Awolaja ya tabbatar da mutuwar marigayin, kamar yadda TVC News ta tattaro.
Martanin dan Majalisa mai wakiltar yankin
Ya ce:
“Na samu labarin rasuwar dattijo Jimi Solanke dazu-dazu, tabbas mutuwarsa babban rashi ne ga Remo ta Arewa da jihar Ogun.
“Babban rashi ne ganin yadda ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban kasarmu baki daya, ubangiji ya yi masa rahama.”
Wannan rashi na zuwa ne kwana ɗaya bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Yobe a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu a kasar Saudiyya.
An binne Bukar Abba a Saudiyya
Kun ji cewa bayan rasuwa tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim an binne shi a kasar Saudiyya.
Marigayin ya rasu ne a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami da ke Makka bayan idar da sallar Asuba.
Asali: Legit.ng