Gwamnan Arewa Ya Rusa Dukkan Ciyamominsa 21 da Sakatarorinsu, Ya Bayyana Dalilin Hakan

Gwamnan Arewa Ya Rusa Dukkan Ciyamominsa 21 da Sakatarorinsu, Ya Bayyana Dalilin Hakan

  • Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya rusa dukkan ciyamomin kananan hukumomi 21 da ke fadin jihar
  • Gwamnan ya kuma sanar da rusa dukkan sakatarorinsu saboda wa’adinsu ya zo karshe a yau Litinin
  • Gwamna Idris ya ce wa’adin nasu ya kare a yau Litinin 5 ga watan Faburairu yayin jawabi a Birnin Kebbi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gwamna Nasir Idirs na jihar Kebbi ya sanar da rusa dukkan ciyamomin kananan hukumomi 21 a jihar.

Gwamnan har ila yau, ya ce dukkan sakatarorinsu ma an rusa su saboda wa’adinsu ya zo karshe.

Gwamnan Arewa ya rusa dukkan ciyamomin kananan hukumomi 21 a jiharsa
Gwamnan Kebbi, Kwamred Nasir Idris Ya Rusa Dukkan Ciyamominsa 21 da Sakatarorinsu. Hoto: Nasir Idris.
Asali: Facebook

Yaushe Idris ya rusa ciyamomi a jihar?

Rusa ciyamomin na zuwa ne bayan wa’adinsu ya kare a yau Litinin 5 ga watan Faburairu da muke ciki, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki gagarumin mataki bayan 'yan bindiga sun kwashe 'yan kai amarya 60

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya umarci ciyamomin da su mika dukkan wasu muhimman abubuwan da ke tare da su ga daraktocin kananan hukumomin.

Yayin da ya ke jawabi ga rusassun ciyamomin a Birnin Kebbi, Idris ya gode musu kan irin gudunmawar da suka bayar.

Ya ce akwai dokoki da aka gindaya kan gudanar da kananan hukumomin inda ya ce dole ne sai ya bi dokokin gaba daya, Premium Times ta tattaro.

Jawabin Gwamna Nasir Idris na Kebbi

Ya ce:

Ya kamata mu yi wani abu saboda daga baya komai ya biyo baya, ba son ranmu ba ne korar wani a kan kujerar.
“Za mu tabbatar ba mu ya da kowa ba, wannan gwamnatinku ne don ya kamata ku ba ta goyon baya don ta samu ci gaba.”

Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da ayyukan alkairi a jihar ga dukkan banmgarorin jihar don cika alkawuran da ya dauka.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya rufe wurin ibada kan damun jama'a da kara, ya gargadi mutane kan saba dokar

Da ya ke jawabi, shugaban kungiyar ciyamomin, ALGON, Aminu Sarkin-Fada ya godewa gwamnan kan goyon baya da ya ba su.

A cewarsa:

“Na tabbata ba tare da goyon bayan mai girma gwamnan ba, da ba mu samu ci gaban da muka yi a yanzu ba.”

Kotu ta yanke hukunci kan zaben Kebbi

Kun ji cewa Kotun Koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kebbi da aka gudanar a jihar.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Nasir Idris a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.