Za a Gamu da Cikas Wajen Gine-Gine, Ma’aikata Sun Tafi Yajin-Aiki Daga Yau

Za a Gamu da Cikas Wajen Gine-Gine, Ma’aikata Sun Tafi Yajin-Aiki Daga Yau

  • Kungiyoyin ma’aikatan gine-gine sun janye aiki har sai nan da tsakiyar mako saboda tsada rayuwa
  • Shugabannin NUCECFWW da CCESSA sun yi zaman majalisar NEC, sun yanke shawarar yin yajin-aiki
  • Gwamnati tayi wa ma’aikata karin albashi, Ibrahim Walama da Tony Egbule sun ce an manta da su

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Ma’aikatan da ke harkar gine-gine a Najeriya sun shiga yajin-aiki na jan-kunne saboda halin matsin rayuwa da ake ciki.

A safiyar Litinin, Daily Trust ta rahoto cewa ma’aikatan za su yi kwanaki uku ba su aiki domin su koka da yanayin albashinsu.

Yajin-aiki
Masu gine-gine sun tafi yajin-aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kuncin rayuwa a Najeriya

Masu harkar gine-gine a Najeriya sun ce duk yadda rayuwa tayi tsada, ba a kara masu kudi a kan abin da suka saba karba ba.

Kara karanta wannan

Najeriya ta sayo jiragen $1bn daga kasar Amurka domin ragargazar ‘yan ta’adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A dalilin wahalar da ake ciki ne gwamnatin Bola Tinubu ta sha alwashin biyan ma’aikata N35, 000 a kowane wata tun daga bara.

NUCECFWW ta masu manyan gine-gine da CCESSA ta manyan ma’aikata sun sanar da shiga yajin-aikin a ranar Juma’ar da ta wuce.

Kungiyoyi sun tafi yajin-aiki

Kungiyoyin sun dauki wannan matsaya ne bayan wani zaman majalisar NEC da aka yi a makon jiya, The Guardian ta fitar da rahoton.

Sanarwar ta ce shugabannin wadannan kungiyoyi sun bukaci duka ‘ya ‘yansu su tafi yajin-aikin gargadi daga ranar 5 ga Junairu.

Idan komai sun tafi daidai, ba za a wuce ranar Laraba ana yajin-aikin ba, aka bukaci ‘yan kungiyar su saurari duk wani karin bayani.

Jawabin ya fito ne ta bakin Sakataren NUCECFWW, Ibrahim Walama da Tony Egbule wanda shi ne sakataren rikon kwarya a CCESSA.

Kara karanta wannan

Mai ba Jonathan shawara ya nunawa Tinubu hanyar farfado darajar Naira kan Dala

Wasu ba su tafi yajin-aikin ba

Akwai ma'aikatan da su da masaniyar wannan yajin-aiki da aka shiga a yau.

Wani mai zanen gine-gine a birnin Abuja ya fadawa Legit cewa tashin farashin kaya yana wahalar da kowa a harkar ta su a yanzu.

Arch. Oladipo Onipede ya ce abin ya ta’azzara a wurinsu, amma wasu irinsa sun yi dace kamfanoninsu sun kara masu albashi.

Idan sauran kamfanoni za su yi haka, Oladipo yana ganin za a samu kara abin da suke biya, za a samu saukin tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng