An Bankado Sabuwar Makarkashiyar da Ake Kullawa Gwamnatin Shugaba Tinubu
- Ƙungiyar FNPP wacce ta ƙunshi ƙwararru da ƴan kasuwa ta bankaɗo wata maƙarƙashiyar da ake ƙullawa gwamnatin Tinubu
- Ƙungiyar ta yi zargin cewa akwai wasu da ke yunƙurin ɓata sunan Femi Gbajabiamila don kawo cikas ga gwamnatin Tinubu
- FNPP ta yi nuni da cewa ana son ɓata sunan shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasar ne muhimmancin da yake da shi
- Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙwararru da ƴan kasuwa a ƙasar nan ƙarƙashin ƙungiyar ‘Forum of Nigerians Professionals in Politics (FNPP)’ sun bankaɗo maƙarƙashiyar da ake ƙullawa gwamnatin Tinubu.
Sun yi zargin cewa wasu marasa kishin ƙasa ne suke ƙulla makarkashiya don karkatar da gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ta hanyar ɓata sunan ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, cewar rahoton Daily Trust.
Sun ce akwai bayanan sirri da ke nuna cewa waɗanda ke da hannu wajen ɓata sunan shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, maƙiyan gwamnatin Tinubu ne da ke da nufin karkatar da gwamnati daga aiwatar da manufofinta da tsare-tsarenta.
Meyasa ake ƙulla maƙarƙashiya kan gwamnatin Tinubu?
Babban kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Cif Okey Ezenwa a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Lahadi, ya ce masu yin hakan suna yi ne saboda sanin muhimmancin da ofishin yake da shi wajen samun nasarar kowace gwamnti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ezenwa, wanda tsohon mataimakin sakataren jam’iyyar adawa ta PDP ne na ƙasa, ya ƙara da cewa maƙiyan gwamnatin Tinubu sun ɗauki ƴan baranda domin su ƙirƙiri zarge-zargen ƙarya kan Femi domin kawo rikicin cikin gida da karya gwamnatin.
Jaridar Vanguard ta ambato wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ƙungiyarmu ta yi nazari kan zarge-zargen da ake yi wa shugaban ma’aikatan, inda muka gano duk ƙage ne na ƙarya waɗanda ba su da tushe da ake ƙullawa da nufin haifar da rashin jituwa a cikin gida da raunana gwamnatin Tinubu.
"Ganin cewa ofishin na da matuƙar muhimmanci ga samun nasarar gwamnatoci a duk faɗin duniya, waɗanda ke ƙulla maƙarƙashiyar raunata gwamnati da kawo cikas a kullum suna farawa ne da munanan hare-hare kan ofishin na shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa."
Shehu Sani Ya Magantu Kan Sukar Gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu, ya bayyana cewa bai kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu tun yanzu ba.
Tsohon sanatan ya yi nuni da cewa akwai sauran lokaci kafin a fara sukar salon mulkin shugaban ƙasar.
Asali: Legit.ng