Dakarun Sojoji Sun Samu Gagarumar Galaba Kan 'Yan Bindiga a Jihar Arewa
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu galaba kan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Yorro ta jihar Taraba
- Sojojin tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro sun yi nasarar tarwatsa maɓoyar ƴan bindigan
- Bayan tarwatsa maɓoyar ƴan bindigan, sojojin sun kuma kuɓutar da wasu mutum da aka yi garkuwa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Taraba - Dakarun sojoji na bataliya ta 114 na sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro a ranar Asabar sun tarwatsa maboyar ƴan bindiga a jihar Taraba.
Dakarun sojojin sun kuma kuɓutar da wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Yorro ta jihar Taraba, cewar rahoton TheCable.
Olabodunde Oni, muƙaddashin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Oni ya ce an fara ɗaukar matakin gaggawa na fatattakar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke kawo cikas ga zaman lafiya a ƙaramar hukumar Yorro da kewaye tun ranar 2 ga watan Fabrairu, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Sojojin sun yi artabu da ƴan bindiga
Ya ce sojojin sun gamu da ƴan bindigan a tsaunin Gampu da yankin Ban Yorro inda suka yi artabu da su.
Bayan haka, ruwan wutan da ƴan bindiga suka sha daga wajen sojojin ya sa suka tsere daga wurin, inda suka bar mutum huɗu da suka sace.
A kalamansa:
"Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da aikin domin tabbatar da cewa an gano sauran waɗanda aka yi garkuwa da su da suka gudu yayin musayar wuta tare da sake haɗa su da ƴan uwansu.
"Waɗanda aka ceto sune, Genesis Samuel, mai shekara 24, daga ƙauyen Ganku, Benard Denis, mai shekara 28, daga ƙauyen Fulfualgon, Esther Titus, mai shekara 35, daga ƙauyen Kosanai da kuma ɗan Sarkin Pupulle, Isma’il Umar, mai shekara 25, wanda aka yi garkuwa da shi a gidansa a ranar 18 ga watan Janairu.
"Rundunar ta himmatu wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama'a da kuma wargaza duk wasu ababen da suka shafi aikata laifuka a jihar."
Sojoji Sun Sheƙe Ƴan Bindiga a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar sheƙe ƴan ta'adda masu yawa a jihar Katsina.
Sojojin sun samu nasara kan ƴan ta'addan bayan sun kai farmaki ta sama da ta ƙasa a maɓoyarsu da ke ƙaramar hukumar Safana ta jihar.
Asali: Legit.ng