Abun Mamaki: An Saka Lemun Tsamin da Ya Shekara 285 a Kasuwa, an Taya Shi Naira Miliyan 1.8
- Mutane sun yi matukar mamakin yadda wani mutum ya taya lemun tsamin da ya shekara 285 a duniya kan naira miliyan 1.8
- Wani gidan gwanjon kayayyaki ne a Ingila ya saka lemun a kasuwa bayan da ya tsince shi a cikin wata dirowar kayayyaki
- A jikin lemun an ga wani sako da ke nuna cewa an ba da kyautar lemun ne a ranar 4 ga watan Nuwamba, shekarar 1739
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An yi gwanjon lemo mai shekaru 285 da aka gano a bayan wata tsohuwar dirowar ajiyar kaya a kan $1,780 (kimanin naira miliyan 1.8) a Ingila.
Wani gidan gwanjon kayayyaki na Brettells a Shropshire sun ce wasu ne suka kawo dirowar saka kayan da aka hada ta tun a karni na 19 a gidan gwanjon.
Wani kwararre ne ke daukar hoton dirowar da zummar sayarwa a lokacin da aka gano lemo a bayan akwakwun dirowar, kamar yadda UPI ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rubuta sako a jikin lemun kamar haka: "Kyauta daga Mista P Lu Franchini a ranar 4 ga watan Nuwamba, 1739 zuwa ga Miss E Baxter."
Gidan gwanjon ya yanke shawarar yunkurin siyar da tsohon lemun, lamarin da ya sa jami’ai suka kadu a lokacin da suka sami wani babban tayin dala 1,780.
Amma ita dirowar an sayar da ita ne akan dala 40 kacal, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kasashe biyar a duniya da rana ba ta faduwa
A wani rahoton na abubuwan ban al'ajabi, Legit Hausa ta tattaro maku bayani kan wasu kasashe biyar da rana takan dauki sama da kwanaki 70 ba tare da fadi ba.
A wasu sassa na duniya kamar Norway, Kanada, Iceland, da Finland, rana na zuwa kusa da Da'irar Arctic, wanda ke sa ta tsaya da haskenta ko da a cikin dare.
Duba jerin kasashen a nan tare da bayanai akan yanayin su.
Kasashe biyar da ya kamata ka ziyarta don bude ido
Har ila yau dai, akwai wasu kasashen duniya biyar da ya kamata a ce ka ziyarta idan ka samu hali don ganin ababen tarihi da ban al'ajabi a yayin da kake yawon bude ido.
Wadannan kasashen na cike da gine-gine, al'adu, abinci da tsarin kasa mai ban sha'awa wanda kuma ke marabtar masu zuwa ci-rani.
Asali: Legit.ng