Gwamnatin Katsina Ta Dauki Gagarumin Mataki Bayan 'Yan Bindiga Sun Kwashe ‘Yan Kai Amarya 60
- Gwamnatin Katsina ta dukufa aikin ceto 'yan kai amarya da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su a yankinDamari dake jihar
- Kwamishinan tsaron cikin gida da rundunar 'yan sandan jihar sun tabbatar da hakan a ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu
- 'Yan bindiga dai sun sace 'yan kai amaryar ne kimanin su 60 a hanyarsu ta zuwa kauyen unguwar Mujiya, karamar hukumar Dandume daga kauyen Gamji,
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa an fara aikin ceto 'yan kai amarya 60 da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da su a garin Damari dake jihar.
Akalla mutane 60 dake yi wa amarya rakiya ne 'yan bindiga suka sace a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Wani mazaunin yankin da ya tabbatar da ci gaban a wata hira da jaridar Punch, ya bayyana cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake magana ta bakin kakakinsa, Tukur Ali, a ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Muazu Nasiru, ya bayyana cewa gwamnati na sane da sace 'yan kai amaryar.
Nasiru ya kuma bayyana cewa an kaddamar da ayyukan tsaro domin tabbatar da ganin an ceto mutanen.
Kwamishinan ya ce:
"Muna sane da batun garkuwa da mutaen a Sabuwa kuma mun kaddamar da ayyukan ceto don tabbatar da wadanda aka sacen sun samu 'yancin su. Nagode."
Rundunar 'yan sanda ta yi martani
A wani sakon waya da yake tabbatar da lamarin, kakakin 'yan sandan jihar, Abubakar Aliyu ya bayyana cewa 'yan bindigan sun sace mata 35, rahoton NewsNow.
Sakon na cewa:
"Wasu da ake zaton 'yan bindiga ne sun sace wasu mata a hanyar zuwa kauyen unguwar Mujiya, karamar hukumar Dandume, daga kauyen Gamji, karamar hukumar Sabuwa, a lokacin da suka isa wani wuri tsakanin Sabuwa da Dandume.
"Sun yi masu kautan bauna tare da yin awon gaba da mata 35."
"Rundunar ta yi amfani da dabarunta na sirri wajen tabbatar da ceto wadanda aka sace ba tare da matsala ba. Za a sanar da karin ci gaba a kan lokaci."
'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro
A wani labarin, mun ji cewa wasu ƴan bindiga biyar da sanyin safiyar jiya sun kai wani mummunan hari a Yantumaki cikin ƙaramar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun kai hari ne gidan wani Malam Suleiman Mai Rake da ke Unguwar Yayyara a Yantumaki, cewar rahoton Vanguard.
Asali: Legit.ng