Mummunar Gobara Ta Lakume Dukiya Na Miliyoyin Naira a Jihar PDP
- Mummunar gobara ta tashi a garin Amarata dake karamar hukumar Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Asabaar, 3 ga watan Fabrairu
- Gobarar da ta fara daga wani gidan mai ta lakume gidaje da shaguna da dama, lamarin da ya kai ga rasa miliyoyin naira
- Lamarin ya samo asali ne daga fashewar wata mota dake dauke da mai da aka tace ba bisa ka'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Wata gobara ta sassafe ta lakume dukiya da kayayyaki na miliyoyin naira a garin Amarata dake karamar hukumar Yenagoa, jihar Bayelsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gobarar wacce ta tashi da misalin karfe 2:30 na daren Asabar, ta fara ne sakamakon tartatsin wuta.
Hakan ya faru ne bayan wata mota dauke da danyen man da aka tace ba bisa ka'ida ba ta fashe a yayin da ake kokarin sauke man a wani gidan mai da ke kusa da yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda gobara ta lakume gidaje da shaguna
Wadanda abun ya ritsa da su da shaidu sun sanar da manema labarai cewa man dizal din da ya kwararo daga motar ne ya kona wani bangare na gidan man.
Hakazalika, wutan ya yadu zuwa wasu gine-gine da shaguna a yankin, inda ya kona gidaje da kayayyakin mutane.
Wata da abun ya ritsa da ita, Ebiomo Queen, wacce ke gudanar da wai dan karamin shago a yankin, ta ce kayayyaki da kudade dake shagonta da suka kai kimanin naira miliyan 20 sun kone bayan ta tashi a daren jiya.
Wani da abun ya ritsa da shi, Mista Theophilus Joseph Otti, ya ce jami'an tsaro daga gidan man Kimiowei dake kusa ne suka ankara da lamarin, kuma ko da suka tashi gobarar ta riga ta fara yaduwa.
Wani mai suna Chinyere Eze, wanda gobarar ta kona masa gida, ya ce bai iya fitar da komai daga gidan nasa ba, yayin da suka dukufa wajen ceto rayuka maimakon dukiya.
Kakakin 'yan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, ya tabbatar da tashin gobarar, Peoples gazatte ta ruwaito.
Gobara: Gwamnatin Zamafara za ta tallafawa 'yan kasuwa
A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi alƙawarin bayar da duk wani tallafi da taimako ga waɗanda gobarar babbar kasuwar Gusau ta shafa.
A daren ranar Talata ne wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Gusau, inda ta yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya da lalata shaguna sama da 50.
Asali: Legit.ng