Dangote Ya Rasa Dala Biliyan 5 Cikin Awanni 24, Ya Sauka Daga Jerin Masu Kudin Duniya 100
- Mai kudin Najeriya, Aliko Dangote, ya sauka daga sosai a jerin attajirai bayan ya rasa naira triliyan 7 cikin awanni 24
- Arzikin Dangote ya ragu bayan karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta sake yi karo na biyu cikin watanni takwas
- Arzikin Dangote ya ragu daga dala biliyan 22 zuwa biliyan 16.6 cikin sa’o’i 24, lamarin da ya sa shi ficewa daga cikin masu kudin duniya 100
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Mai kudin Najeriya da Afrika, Aliko Dangote, ya sauka daga lamba na 81 zuwa 113 a jerin masu kudin duniya cikin awanni 24.
Lamarin ya biyo bayan rasa dala biliyan 5.4 (naira triliyan 7) da mai kudin Najeriyan ya yi a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairun 2024.
Arzikin Dangote ya rage cikin awanni 24
Dangote ya sauka ne yayin da kasuwar hada-hadar kudi ta Najeriya (NGX) ta yi asarar biliyoyin kudi bayan shafe makonni biyu ana tafka tsadar dala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkaluman kididdigar attajirai na Bloomberg sun nuna cewa dukiyar Dangote ta ragu daga dala biliyan 22 zuwa dala biliyan 16.6 a cikin awanni 24.
Dangote ya samu dala biliyan 7.11 a watan Janairu, biyo bayan kokarin da kamfanin simintin Dangote ya yi, wanda ya tashi ya zama babban kamfani a Najeriya wanda darajarsa ya kai naira tiriliyan 13.
Najeriya ta sake rage darajar naira
Masu nazari sun kuma dora alhakin faduwar darajar kudin Dangote kan rage darajar naira da gwamnatin Najeriya ta yi a baya-bayan nan.
An rahoto cewa gwamnati ta karya darajar naira a karo na biyu cikin watanni takwas yayin da take fafutukar kawar da rudanin canjin da ake samu da kuma jawo hankalin masu zuba jari na kasashen waje.
Darajar naira ta ragu sosai a makon karshe na watan Fabrairun 2024 a hukumance bayan FMDQ ta sauya tsarin da ake amfani da shi wajen kididdige farashin canji a hukumance, inda ta kai ta kusa da farashin kasuwar bayan fage.
Ana kallon matakin a matsayin wani gyara na kasuwanci da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar, wanda ya fitar da naira sosai jim kadan bayan ya zama shugaban kasa a watan Mayun 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa, sabon tsarin ya sauya farashin canji a hukumance daga N900 zuwa kusan N1,500 kowacce dala.
Arzikin Dangote ya karu
A baya mun ji cewa darajar hannun jarin kamfanin simintin Dangote ya ya karu ba da wasa ba.
Kan haka ne arzikin Alhaji Aliko Dangote ya karu zuwa fam $22bn kamar yadda Bloomberg ta ruwaito.
Asali: Legit.ng