Dukiyar Talakawa: EFCC Ta Yi Nasarar Kwato Zunzurutun Kuɗi Samada N70bn Cikin Kwana 100

Dukiyar Talakawa: EFCC Ta Yi Nasarar Kwato Zunzurutun Kuɗi Samada N70bn Cikin Kwana 100

  • Hukumar da ke yaƙi da barayin dukiyar ƙasa EFCC ta kwato makudan kuɗaɗe daga masu laifi a cikin kwanaki 100 kaɗai
  • A wata takarda da ta bayyana, EFCC ta samu nasarar dawowa da kuɗin da aka sace da suka kai kimanin Naira biliyan 70
  • Bayan haka hukumar ta karbi korafe-korafe sama da 2000 sannan ta yi nasarar hukunta masu laifi 747 a gaban kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta ce ta kwato jimillar N70,556,658,370.5 cikin kwanaki 100, tsakanin Oktoba 2023 zuwa 19 ga Janairu, 2024.

Punch ta ce cikakken bayanin wannan nasara da EFCC ta samu na kunshe ne a wata takarda da hukumar ta yi wa taken, "ayyuka da kuma nasarar dawo da dukiyar kasa."

Kara karanta wannan

Babban nasara: Sojoji sun sheke 'yan ta'adda 185, sun kama wasu 212

Hukumar EFCC.
Hukumar EFCC Ta Kwato Naira Biliyan 70 Cikin Kwanaki 100, Rahoto Hoto: EFCC
Asali: Twitter

Takardar ta bayyana cewa a tsakanin watan Oktoba 2023 zuwa 19 ga Janairu, 2024, EFCC ta kwato N60,969,047,634.25, $10,522,778.57, £150,002.10, da kuma €4,119.90.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan aka haɗa jumullar kudin kuma aka sauya su zuwa kuɗin mu na gida Najeriya sun kama Naira biliyan N70,556,658,370.5, sune EFCC ta kwato a kwana 100.

EFCC ta karɓi dubban ƙorafe-ƙorafe a kwanaki 100

Bugu da ƙari, a tsawon wannan lokaci hukumar EFCC mai yaƙi da marasa gaskiya ta samu korafe-ƙorafe 3,325 daga al'umma wanda daga cikinsu ta aminta da guda 2,657.

Haka nan kuma hukumar ta gurfanar da mutane 747 a gaban ƙuliya kuma an hukunta su bisa laifin da suka aika kamar halasta kudin haram da damfarar yanar gizo.

A bayanan da ke kunshe a takardar wannan ayyuka, hedkwatar EFCC da ke Abuja kaɗai ta samu nasarar kwato N49,607,391,330.44, $3,900,200.75, £2000, da kuma £110.

Kara karanta wannan

Jerin kasashen duniya 5 da ya kamata ka ziyarta kafin su kara yawan jama'a

Wasu mutane sun sace arzikin Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa Shehu Sani ya bayyana yadda wasu mutane suka sace arzikin Najeriya a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Buhari.

Sanata Sani ya yi iƙirarin cewa waɗanda Buhari ya aminta ya naɗa a muƙamai sun yi kashe mu raba da dukiyar baitul mali kuma sun gurgunta makomar ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262