'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da 'Mata 55' Ƴan Kai Amarya a Jihar Arewa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da 'Mata 55' Ƴan Kai Amarya a Jihar Arewa

  • Miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da gomman mata ƴan kai amarya a jihar Katsina ranar Alhamis da daddare
  • Rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan sun sace matan ne bayan sun harbi diraban babbar motar da suke ciki
  • Shugaban ƙaramar hukumar Ɗandume, Alhaji Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Tsagerun ƴan bindiga sun yi awon gaba da mata kusan 55 yan raka amarya har ɗakin aurenta a titin zuwa Damari, karamar hukumar Sabuwa a Katsina.

Sai dai har kawo yanzun hukumomin tsaro ba su fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba.

Yan bindiga sun yi garkuwa da ƴan kai amarya a Katsina.
Miyagun ƴan Bindiga Sace Ƴan Kai Amarya Mutum 55 a Jihar Katsina Abin lura: An yi amfani da wannan hoton ne domin yin nuni
Asali: Getty Images

Amma wani mazaunin yankin ya shaida wa Channels tv ta wayar tarho cewa lamarin ya auku ne ranar Alhamis da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kai farmaki wurin taron murnar nasarar gwamnan PDP a Kotun Ƙoli, sun tafka ɓarna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ƴan banga uku sun rasa rayukansu a kokarin ceto tawagar ƴan kai Amaryan daga hannun ƴan ta'adda.

"Gabanin ƴan bindiga su farmake su, ƴan raka amaryan sun haura mutum 70 a cikin mota mafi akasari ƙawayen amarya ne, amma da yawa daga ciki sun tsira daga harin."

Yadda lamarin ya auku

A rahoton Vanguard, akalla mata 30 ne ƴan kai amarya suka faɗa tuggun ƴan bindiga titin Gamji da ke ƙaramar hukumae Ɗandume a Katsina.

Tawagar matan na kan hanyar zuwa kai amarya a cikin babban motar ɗaukar kaya kwatsam ƴan bindiga suka musu kwantan ɓauna da misalin ƙarfe 8:30 zuwa 9:00 na dare.

Wata majiyar yankin ta bayyana cewa maharan sun harbi direban motar kuma yanzu haka yana kwance yana jinya a asibitin Damari.

Ciyaman ya bayyana halin da ake ciki

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaro a Arewa, sun halaka mutum 4

Shugaban ƙaramar hukumar Ɗandume, Alhaji Basiru Musa, ya tabbatar da faruwar lamarin garkuwa da mutanen.

Ya kuma bayyana cewa matan mazauna garin Dandume ne kuma an sace su ne a lokacin da suke dawowa daga karamar hukumar Sabuwa da misalin karfe 9:00 na dare.

A cewarsa, ana raɗe-raɗin wasu daga cikin matan sun tsero daga hannun ƴan bindigan, yana mai cewa zai bincika ya tabbatar da gaskiyar labarin.

Ƙananan hukumomin Sabuwa da Dandume na yawan fuskantar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Wani maazaunin yankin, Haruna Tukur, ga shaida wa Legit Hausa cewa lamarin ya faru ne a kusa da garinsu kuma ya koka kan rashin ɗaukar matakin gwamnati.

Ya ce:

"Wallahi a kusa da mu abun ya faru, maharan sun sace mata da yawa, nidai ba zan iya cewa ga adadinsu ba kuma har yanzun gwamnati ba ta yi komai ba.
"Mun san Dikko yana kokari amma sai an ƙara tashi tsaye kan mutanen nan, ko a jiya sun tare wata mota, suka kashe direba sannan suka tafi da fasinjojin dukka."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wani abu mara dadi ya auku a jihar Katsina

Sojoji sun kwato mutun 3 a jihar Taraba

A wani rahoton na daban Sojojin Najeriya sun yi artabu yan bindiga, sun kwato mutum uku da suka sace a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

A wata sanarwa da rundunar Birged ta 6 ta fitar, ta ce sojojin sun tari ƴan ta'addan ne bayan tattara sahihan bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262