Najeriya Ta Sayo Jiragen $1bn Daga Kasar Amurka Domin Ragargazar ‘Yan Ta’adda

Najeriya Ta Sayo Jiragen $1bn Daga Kasar Amurka Domin Ragargazar ‘Yan Ta’adda

  • Yunkurin kawo karshen ta'addanci da tsagerancin 'yan bindiga a jihohin Najeriya ya yi nisa a yanzu
  • Ana daf da kammala yarjejeniyar sayen makamai a tsakanin gwamnatin tarayya da kasar Amurka
  • Sojojin Najeriya za su samu jiragen AH-1Z masu saukar ungulu wadanda suka yi fice a barin wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

America - Ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta tabbatar da ciniki tsakaninta da Najeriya domin magance matsalar ta’addanci.

Leadership ta kawo rahoto a yammacin Alhamis cewa Amurka ta saida wasu jirage 12 na AH-1Z masu saukar ungulu ga Najeriya.

Jirage
Jiragen yaki daga Amurka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/www.military.africa
Asali: Facebook

Mummunan matsalar tsaro a Najeriya

Hakan zai taimakawa kasar Afrika ta yamman wajen yakar ‘yan ta’adda da kuma miyagun ‘yan bindiga da suka addabi al’ummarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan cin karfin ta’addancin Boko Haram a Arewa maso gabas, yanzu ana fama da ‘yan bindiga da ke ta’adi suna karbar kudin fansa.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da gobara ta kama gadan-gadan a wata babbar coci a Najeriya

Rahoton ya ce wannan kwangilar ta $1bn ta kunshi wadannan manyan jirage masu saukar ungulu da gafaka watau komfutoci 32.

Kamfanin Northrop Grumman ya samar da na’urori masu kwakwala a kan $7.7m bayan yarjejeniyar da aka yi a Disamban bara.

Yarjejeniya da Muhammadu Buhari

Zuwa watan Yunin 2024 ake sa ran a kammala wannan ciniki domin bunkasa kayan yakin da jami’an tsaro su ke da su a Najeriya.

A baya an rika samun badakala a gwamnatin Najeriya wajen sayen makamai.

Tun a shekarar 2022 sakataren gwamnatin Amurka ya amince da bukatar Najeriya na sayen wadannan manyan jiragen yaki.

Bayani a kan jiragen AH-1Z

Jiragen AH-1Z suna iya aiki cikin dare kuma ana amfani da su wajen horas da sojoji.

Bayan aiki komai duhun dare, jiragen masu saukar ungulu sun yi fice wajen luguden wuta da na’urar AAM daga sararin samaniya.

Ana sa ran Najeriya za ta samu jiragen m-346 da T-129 ATAK da kirar Agusta 109 Trekker da kuma jiragen Sin marasa matuka.

Kara karanta wannan

N200,000 tayi kadan: ‘Yan kwadago sun yanke albashin da suke so a koma biyan ma’aikata

Nasarar jami'an tsaro a Kaduna

An rahoto Air Vice Marshal Edward Gabkwet yana bayyana nasarar da sojojin sama suka samu a wani hari da suka kai a Birnin Gwari.

Marshal Edward Gabkwet ya ce sojoji sun ji labarin motsin ‘yan ta’adda a kan babura, a nan take suka kashe su da aka buda masu wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng