Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu San Da Wani Kwangilar Siyan Makamai Na $875m Daga Amurka Ba, FG

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Mu San Da Wani Kwangilar Siyan Makamai Na $875m Daga Amurka Ba, FG

  • Gwamnatin Nigeria ta karyata cewa yan majalisar Amurka na neman hana a siyar mata makaman yaki na kudi $875m
  • Ministan Labarai Lai Mohammed ya karyata rahoton da ya fito cewa yan majalisan sun hana a siyar da makaman saboda zargin keta hakkin bil adama
  • Lai Mohammed ya ce labarin karya ne kuma babu wata kwangilar makamai tsakanin Nigeria da Amurka ila na Tucano wanda tuni wasu jiragen sun iso

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce ba ta san da wani zancen kwangilar siyan makaman yaki na $875m tsakaninta da kasar Amurka ba, Daily Trust ta ruwaito.

A baya, Legit.ng Hausa ta ruwaito matakin da yan majalisar Amurka suka dauka game da batun siyarwa Nigeria jiragen yaki masu saukan Angulu na 12 AH-1 Cobra da wasu kayayaykin tsaro.

Reuters ta ambaci majiyoyi uku na cewa an fasa sayar da makaman ne saboda damuwa kan take hakkin bil adama da gwamnatin tarayyar Nigeria ke yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta nemi a dauki tsatsauran mataki kan masu safarar mutane da sauransu

Da Dumi-Dumi: Ba Mu San Da Wani Kwangilar Siyan Makamai Na $875M Daga Amurka Ba, FG
Ministan Labarai Da Al'adu, Lai Mohammed. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rahoton kwangilar siyan makaman labarin karya ne - Lai Mohammed

Amma a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, a ranar Juma'a, a Abuja, Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana labarin a rahoton a matsayin 'labarin karya'.

Ministan ya ce ba bu wani kwangila irin wannan tsakanin Nigeria da Amurka.

A cewar Lai Mohammed:

"Babu wata kwangilan siyan makamai tsakanin gwamnatin tarayyar Nigeria da Amurka a yanzu ila na siyan Super Tucano 12 wanda tuni guda shida cikinsu sun iso Nigeria."
"Mun gamsu da yanayin aiki da hadin kai da muke samu daga gwamnatin Amurka a kan wannan batun.
"Maganan gaskiya ma shine za a kaddamar da jiragen yaki na Tucano a Agustan wannan shekarar.
"Ba mu san wani kwangilan dalla miliyan 875 ba ko wasu jirage masu saukan ungulu da yan majalisar Amurka ke kokarin hana shugaban kasar ya sayar mana.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro a Najeriya: Ministan tsaro Magashi ya bayyana sunayen wadanda za a zarga

"Akwai kyakyawar alaka tsakanin Nigeria da Amurka."

Jiragen Yaƙin Tucano 6 Da Najeriya Ta Saya Daga Amurka Sun Iso Nigeria

Rundunar sojojin saman Nigeria, NAF, a ranar Alhamis ta karbi rukuni na farko na jiragen sama na yaki kirar A-29 Super Tucano daga kasar Amurka.

Edward Gabkwet, direktan sashin hulda da jama'a da watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin saman Nigeria da ke Abuja ne ya sanar da hakan.

Bashir Magashi, Ministan tsaro; Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa; da Oladayo Amao, babban hafsan sojojin sama ne suka karbi jiragen a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164