Innnalillahi: Kashim Shettima Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

Innnalillahi: Kashim Shettima Ya Yi Babban Rashi a Rayuwarsa

  • Matataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi rashin matar mahaifinsa wacce ta rigamu gidan gaskiya
  • Hajja Hauwa Abba Kormi ta rasu tana da shekara 69 a duniya bayan ta ɗauki dogon lokaci tana jinyar rashin lafiya
  • Babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasan ne ya sanar da rasuwarta a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a safiyar ranar Alhamis, ya rasa matar mahaifinsa, Hajiya Hauwa Abba Kormi, wacce ta rasu.

Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban ƙasan kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar a shafinsa na X ta ce Hajia Kormi ta rasu ne bayan doguwar jinya.

Kara karanta wannan

Atiku ya bayyana ƴan takarar da yake goyon baya a zaben da za a yi ranar Asabar a jihohi 9

Matar mahaifin Kashim Shettima ta rasu
Matar mahaifin Kashim Shettima ta rigamu gidan gaskiya Hoto: Kashim Shettima
Asali: Twitter

A cewar sanarwar marigayiyar ta rasu tana da shekara 69 a duniya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"A safiyar yau ne mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, GCON, ya rasa matar mahaifinsa Hajja Hauwa Abba Kormi.
"Hajja Kormi wacce ta rasu bayan doguwar jinya tana da shekaru 69, ta bar ƴaƴa biyar, ƴaƴan miji da jikoki.
"An shirya Janaizarta da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a yau a Shettimari, Lawan Bukar, Maiduguri, jihar Borno.
"Allah ya gafarta mata kurakuranta, ya shigar da ita Jannatul Firdaus".

Ƴar uwar Jonathan ta rasu

Tsohon shugaban ƙasa Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya rasa babbar yayarsa wacce ta rigamu gidan gaskiya.

Madam Obebhatein Jonathan wacce ta rasu tana da shekara 70 a duniya, ta yi fama da ƴar gajeruwar jinya a babban asibitin tarayya FMC da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Babban labari: An rantsar da sabon mataimakin gwamnan jihar APC, sahihan bayanai sun fito

Mai Magana da Yawun Zulum Ya Rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa cewa mai magana da yawun Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, Mallam Isa Gusau, ya rasu a wani asibiti da ke ƙasar Indiya.

Gusau shine mai magana da yawun Kashim Shettima, a lokacin da ya ke gwamna a jihar Borno. Kakakin na Zulum ya shafe kimanin wata guda a wani asibiti a Indiya yana jinyar wani ciyo da ba a bayyana ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng