Yan Bindiga Sun Kuma Kai Farmaki Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Mutane da Dama

Yan Bindiga Sun Kuma Kai Farmaki Wata Jihar Arewa, Sun Kashe Mutane da Dama

  • Yan bindiga sun farmaki wasu kauyukan jihar Taraba a ranar Laraba, inda suka kashe mutane uku tare da jikkata wasu
  • Mazauna garuruwan sun labarta cewa 'yan bindigar sun farmake su ne sanye da kayan sojoji dauke da muggan makamai
  • Garuruwan da 'yan bindigar suka kai wa hari sun hada da Akinde, Tse Yongo, Tse Adem da Tse Ahikyegh da ke Donga a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Taraba - Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba sun kai hari a kauyukan Akinde, Tse Yongo, Tse Adem da Tse Ahikyegh a karamar hukumar Donga a jihar Taraba.

Harin ya kai ga kisan mutane uku yayin da mazauna yankin da dama suka samu raunuka daban-daban na harbin bindiga, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A kara hakuri: Minista ya ce ana daf da cin moriyar kudurorin Shugaba Tinubu a Najeriya

Yan bindiga sun kai farmaki Taraba
Yan bindiga sun kai farmaki wasu kauyukan Taraba, sun kashe mutum uku. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Yan bindigar na sanye da kayan sojoji

Wani shugaban Ugondo, Zaki Uma Ugondo, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa suna zargi wasu kamar sojoji ne tare da mayakan Jukun suka kai farmakin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaki Ugondo ya ce da yawan 'yan bindigar na sanye da kakin sojoji, kuma suna haye kan babura na sojoji sa'ilin da suka farmaki kauyukan.

Ya ce:

“Sun zo ne a kan babura na sojoji sama da 30 yayin da yawancin su ke sanye da kakin soja, kuma suna dauke da muggan makamai.
"Da farko da mutanen kauye suka gansu, sai suka yi zaton sojoji suka zo, ba tare da sanin cewa 'yan bindiga ne da za su kashe su ba."

Yan bindigar sun kashe mutane uku

Ya shaida cewa, 'yan bindigar sun fara mamaye garin Akinde kafin su wuce zuwa Tse Yongo, sannan suka je Tse Adem da kuma Tse Ahikyegh.

Kara karanta wannan

Kudin Fansa: Masu garkuwa suna barazanar hallaka mutanen Abuja 11 da aka sace

Zaki Ugondo ya bayyana cewa sun kashe Luper Unongo, Tony Yongo da Gerigori Akinde, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Yan bindiga sun kashe matar dan sanda a Neja

A wani labari , wasu 'yan bindiga sun kashe matar wani dan sanda tare da surukarsa a karamar hukumar Tafa da ke jihar Neja.

Da farko 'yan bindigar sun fara yin garkuwa da matar, jaririnta da mahaifiyarta, inda suka nemi kudin fansa, amma gaza biyan kudi ya sa suka kashe matan biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.