Gwamnan PDP Ya Sa a Kama Fitaccen Malamin Musulunci a Arewa? Gaskiya Ta Bayyana
- Gwamnatin Bauchi ta musanta hannun Gwamna Bala Mohammed a cafke fitaccen malamin nan, Sheikh Idris Dutsen-Tanshi
- Malamin mai ikirarin bin tafarkin aƙidar Sunnah na fuskantar shari'a a gabm kotu wanda ya kai ga kulle shi a gidan Kurkuku
- Kwamishinan albarkatun ruwa na Bauchi, Abdulrazaq Nuhu Zaki, ya ce ƴan sanda na kokarin sake kama malamin ne kan rashin zuwa zaman kotu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin Gwamna Bala Muhammed ta musanta cewa ita ta sa aka cafke babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen-Tanshi, Dakta Idris Abdul’aziz.
Sheikh Dutsen-Tanshi, mai bin aƙidar Sunnah ya shiga hannu ne biyo bayan wasu kalamai da ya yi kan ƙimar Manzon Allah, Annabi Muhammad SAW a karatunsa.
Bisa rashin jin daɗin kalaman malamin mai yawan haddasa ruɗani, wasu ƙungiyoyin musulmai karƙashin Fityanul Islam suka kai ƙorafi ga kwamishinan ƴan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙorafin da suka shigar gaban CP, sun yi zargin cewa kalaman nasa cin mutunci ne ga Annabi da kuma manyan shehunnan Ɗariqa, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Bayan bincike, rundunar ƴan sanda ta gurfanar da Sheikh Abdul'aziz a gaban kotu kan tuhumar tunzura jama'a, inda aka kulle shi amma daga baya aka bada belinsa, Daily Post ta tattaro.
Shin Kauran Bauchi na d asa hannu a kama malamin?
Da yake zantawa da ƴan jarida jiya Laraba, kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Bauchi, Abdulrazaq Nuhu Zaki, ya ce ba ruwan gwamnatin Bala Muhammed a lamarin.
Kwamishinan ya ce ƴan sanda na yunƙurin sake cafke limamin ne saboda ya yi kunnen uwar shegu da umarnin kotu na kai kansa gabanta.
Ya ce duk da babban malamin ya taimaka wajen nasarar PDP a zaben 2019, amma ya maida filin karatuttukansa wurin cin mutuncin jagorori da malamai masu fahimtar da ta saɓa ta shi.
Zaki ya yi kira ga limamin da ya guji amfani da iliminsa wajen haifar da rashin jituwa a tsakanin mabiya mazhabobi daban-daban da sunan wa'azin akidar Sunna.
Majalisar Kogi ta amince da naɗe-naɗen sabon gwamna
A wani rahoton kuma Majalisar dokokin jihar Kogi ta tabbatar da naɗin sabbin kwamishinoni 18 waɗanda sabon gwamnan jihar ya aiko mata.
A wani lamari da ba a taɓa tsammani ba, Gwamna Ododo ya sanar da naɗin kwamishinonin a jawabinsa na bikin rantsarwa.
Asali: Legit.ng