Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Ministan Tinubu Ya Bukaci Cire Na Wutar Lantarki, Ya Fadi Dalilai
- Ministan Makamashi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya basukan kudaden tallafin wutar ko a zare tallafin a bangaren
- Adebayo Adelabu ya bayyana haka ne a jiya Laraba 31 ga watan Janairu inda ya ce basukan na jawo cikas a samar da wutar
- Ya kara da cewa, a duk fadin Nahiyar Afirka ta Yamma, Najeriya ce ke biyan mafi karancin kudin wutar lantarki
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Ministan Makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu ya nuna damuwa kan matsalar wutar lantarki a kasar.
Adelabu ya danganta matsalar da yawan basukan tallafi inda ya ce dole a sauya salo idan har gwamnati ba za ta iya biyan kudaden ba.
Wace shawara Ministan ya bayar?
Ya ce dole a ta cire tallafin wutar gaba daya idan har ba za a iya biyan kudaden tallafi ba da ‘yan kasuwar ke bi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba 31 ga watan Janairu yayin kai ziyara kamfanin wuta na Olorunsogo a jihar Ogun, cewar Arise News.
Ya ce:
Muna rokon Gwamnatin Tarayya idan har akwai alkawarin tallafi, to dole a biya su gaba daya.
“Idan har gwamnatinmu ba ta shirya biyan kudaden tallafin ba to ya zama dole sai an cire tallafi a bangaren wutar lantarki.
“Da zarar su na bin bashi, to ba za su iya biyan kudaden siyan gas ba wanda hakan zai kara jawo matsala a samar da wutar a kasar.”
Matakin da ake dauka don biyan basukan
Adelabu ya ce ya yi zama da Ministan Kudade da kuma na ma’aikatar kasafi da tsare-tsare don neman hanyar biyan kudaden, cewar Leadership.
Ya kara da cewa, a duk fadin Nahiyar Afirka ta Yamma, Najeriya ce ke biyan mafi karancin kudin wutar lantarki.
Ministan ya ce kasashe kamar su Ghana da Nijar da Ivory Coast su na biyan kusan ninkin kudaden da ‘yan Najeriya ke biya.
NAHCON ta rage kudin aikin hajji
Kun ji cewa Hukumar jin dadin Alhazai ta sanar da rage kudaden aikin hajjin bana idan aka kwatanta da na 2023.
Hukumar ta ce an samu ragin kudaden ne da kaso mai tsoka a bangaren kudin tikiti da masauki da sauransu.
Asali: Legit.ng